Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya ce gwamnatin jihar za ta yi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da ganin jama’ar jihar sun dauki bindiga sun kare kansu daga hare-haren ’yan bindiga.
Gwamnan ya bayyana cewa kare kai dabi’a ce ta dan Adam kuma gwamnatinsa za ta yi duk mai yiwuwa domin ta sauke nauyin da ke kanta na kare rayuwa da kukiyoyin jama’a daidai da abin da doka ta tanada.
- Yadda za ka mallaki lasisin bindiga a Zamfara
- Gwamnatin Zamfara ta umarci mutane su mallaki bindigogi
- Sojoji sun yi tir da umarnin Gwamnan Zamfara cewa mutane su dauki bindiga
Gwamna Matawalle ya ce, “Muna sane da adawar mutane kan matakan da muka dauka, musamman cewa jama’ar yankunan da ’yan bindiga suka addaba, suke hana su harkokinsu na yau da kullum, cewa su ma su dauki bindigogi su kare kansu da al’ummarsu.”
Ya bayyana haka ne bayan kurar da ta taso bayan ya bukaci Zamfarawa su mallaki bindigogi su kare kansu, ya kuma umarci hukumomin ’yan sandan jihar su ba da lasisin mallakar bindiga ga masu bukata a jihar.
A cewarsa, yin hakan ya zama wajibi kuma bai saba tanade-tanaden dokar kasa ba, hasali ma mara wa jami’an tsaro baya ne a kokarinsu na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’ar jihar.
A ranar Litinin Aminiya ta rawaito Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Lucky Irabor, yana cewa matakin babu wata hikima a ciki, domin jami’an tsaro na yin abin da ya kamata wajen shawo kan matsalar tsaro a Jihar Zamfara.
Amma Gwamna Matawalle ya ce, “Muna sane cewa jami’an tsaro na yin bakin kokarinsu wajen yakar wannan matsala, amma suna samun cikas saboda karancin kayan yaki na zamani da kuma karancin ma’aikata.
“Shi ya sa muka karfafi mutanenmu su hada kai su ba da karin gudummawa a kan wanda jami’an tsaron ke yi wajen yakar ’yan bindiga da masu yi musu leken asiri.”
Ya yi wannan jawabi ne a lokacin da yake kaddamar da wasu kwamitoci hudu da ya kafa kan harkokin tsaro a wani bangare na sabon matakan da ya dauka domin yakar ’yan bindiga.
Ya shaida wa taron cewa bukatar mutane da yawa da mallaki bindigogi su kare kansu “ba zai taba sa ba wa tanade-tanaden Dokar Makamai ta Kasa ba.”
Gwamnatin jihar ta ce kafa kwamitocin na daga cikin yunkurinta na yakar ayyukan ’yan bindiga a jihar da ma wasu jihohin Arewacin Najeriya da kuma yankin kasar Jamhuriyar Nijar.
Kwamitocin sun hada da na tara bayannan sirri kan ayyukan ’yan bindiga da kwamitin gudanar da jami’an tsaron sa-kai na jihar da kwamitin hukunta laifuka masu alaka da ’yan bindiga da kuma Kwamitin Tsaro na Jiha.
A lokacin taron, gwamnan ya mika wa kwamitocin sabbin motoci 20 kirar Toyota Hilux da kuma babura 1,500 domin gudanar a ayyukansu.