✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babu Flying Eagles a cikin kungiyoyin da Buhari zai karrama a makon gobe

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana aniyarsa ta karrama ’yan kwallon Najeriya da ke wasa a mataki daban-daban.  kungiyoyin da zai karrama sun hada da…

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana aniyarsa ta karrama ’yan kwallon Najeriya da ke wasa a mataki daban-daban.  kungiyoyin da zai karrama sun hada da kungiyar kwallon kafa na matasa na ’yan kasa da shekara 17 (U-17) da aka fi sani da Golden Eaglets da kuma ta ’yan kasa da shekara 23 (U-23). Sai dai an nuna babu kungiyar kwallon kafa ta Fyling Eagles a cikin wadanda za a karrama.
Ita dai gungiyar Golden Eaglets shugaban zai karrama ta ne saboda nasarar lashe gasar cin kofin duniya na matasa da ya gudana a bara a Chile yayin da  zai karrama kungiyar U-23 ne saboda lashe gasar cin kofin matasa na Afirka a 2015.
Sai dai duk kokarin da kungiyar kwallon kafa ta Flying Eagles ta yi na lashe gasar cin kofin Afirka na matasa a karo na bakwai a watan Maris na 2015,  ba ta cikin wadanda shugaba Buhari ya nuna zai karrama.
Wata majiya ta ce wasu daga cikin kungiyoyin da za a karrama sun hada da kungiyar wasan dara (Scabble) ta Najeriya da ta lashe gasar Dara ta duniya a bara da kuma kungiyar kwallon kwando ta kasa (Basketball) da ake wa lakabi da D’Tigers.
kungiyar Flying Eagles wacce ke karkashin hoarwar Koci Manu Garba ce ta samu nasarar lashe gasar cin kofin matasa na Afirka a Dakar Senegal, bayan ta lallasa Senegal da ci 1-0 a watan Maris, 2015.
Za a gudanar da bikin karrama kungiyoyin  ne a ranar 21 ga watan nan da muke ciki a Abuja.
A wajen bikin ne ake sa ran Shugaba Muhammadu Buhari zai cika alkawarin da ya yi wa ’yan kwallon Golden Eaglets na shekarar 1985 da suka  lashe gasar cin kofin duniya na matasa a wancan lokaci da yake shugaban kasa.