Uwar gidan shugaban kasa, Aisha Buhari, ta ce daga yanzu babu bukatar shugabannin kasar Najeriya su fita kasashen waje domin duba lafiyarsu.
Aisha Buhari ta bayyana haka ne bayan da Shugaba Buhari ya kaddamar da sabon sashen duba lafiyar shugaban kasa da aka gina a asibiti a fadar shugaban kasa da aka kashe wa Naira biliyan 21.
Da take bayanj a wajen bikin, ta shaida wa manema labarai na fadar shugaban kasa cewa an samar da asibitin shekara shida da ta gabata, bayan da maigidanta ya jima yana zaman jinya a kasar waje.
- Kwankwaso ne ya fara sayar da kadarorin Gwamnatin Kano —Ganduje
- El-Rufai zai rushe kamfanoni 9 mallakar Makarfi
Uwar gidan shugaban kasar ta ba da tabbacin cewa samar da asibitin ya wadatar da shugabannin Najeriya da iyalansu bukatar fita waje neman magani ba, amma za su iya fita waje ne kawai don taimaka wa abokan aikinsu a kasashen waje.
A baya dai shugaba Buhari lokacin da yake yakin neman zabensa, ya sha alwashin kin fita waje don neman lafiya, amma hakan ba ta samu ba.
Ya kuma kaddamar da sabon sashen duba lafiyar shugaban kasar ne kwanaki 10 kafin ya sauka daga mulki.