✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babu batun yi wa manyan sojoji ritaya — DHQ

An yi hasashen za a yi wa akalla janar din soji 30 ritaya daga aiki.

Shalkwatar Tsaro ta Najeriya (DHQ), ta yi watsi da jita-jitar da ke yaduwa ta cewa za a yi manyan janar-janar na soji sakamakon nada sabon Babban Hafsan Rudunar Sojin Kasa na kasar.

Ana iya tuna cewa, a kwanakin baya-bayan ne rahotanni suka rika yaduwa kan cewa za a yi wa akalla janar din soji 30 ritaya daga aiki.

Hakan na zuwa ne yayin da wadu ke ganin cewa akwai janar-janar da suka riga Manjo-Janar Farouk Yahaya shiga aikin soji, lamarin da ya sanya aka rika hasashen cewa sojojin da ke gabansa ta fuskar mukami za su ajiye aikinsu bisa al’adar aikin sojin kasar.

Sai dai a jawabinsa ga manema labarai ranar Alhamis a birnin Abuja, Mai magana da yawun Shalkwatar Tsaron, Birgediya-Janar Bernard Onyeuko, ya ce wannan hasashen ba gaskiya bane.

A cewarsa, a halin yanzu babu batun yi wa manyan sojojin ritaya sai dai ga wadanda suke da muradin ajiye aikin don ra’ayi na kashin kansu.

Haka kuma, ya ce manyan sojin da ba su ritayar ba akwai yiwuwar dawo da aikinsu Shalkwatar Tsaron ko kuma a tura su jagoranci a wasu cibiyoyin tsaro na kasar wanda yin hakan duk ya danganta da yadda Majalisar Zartarwa da dakarun tsaron ta yi ra’ayi.

“A wannan gaba, kuna da sanin cewa nadin Manjo-Janar Farouk Yahaya a matsayin Babban Hafsan Sojin Kasa ya tayar da jita-jitar ritaya ta manyan hafsoshin soji a kafofin sadarwa.

“A kan haka ne na ke son na yi amfani da wannan dama don yin watsi da jita-jitar wacce ba ta da asali ballantana tushe.

“A wannan lokaci, babu batun yi wa manyan sojoji ritaya, sai dai hakan ba zai hana duk wanda yake da sha’awar ajiye aikinsa ba a cikinsu, inji Janar Onyeuko.