✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babu abin da zai wargaza Najeriya —IBB

Burina shi ne ganin Najeriya ta zama kasa mai karfi da yalwar arziki.

Tsohon Shugaban Najeriya, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (mai ritaya), ya ce babu abin da zai wargaza kasar duk da irin matsalolin da take fuskanta.

Dangane da bikin cikar Najeriya shekaru 62 da samun ’yanci da za a yi a ranar Asabar, Janar Babangida ya yi wannan jawabi ne yayin zantawa da manema labarai a Minna, babban birnin Jihar Neja.

Tsohon Shugaban Kasar ya shawarci al’ummar Najeriya da su ci gaba da kasancewa masu kwarin gwiwa da yi wa kasar kyakkyawan fata, yana mai mai cewa kasar za ta ci gaba da kasancewa dunkulalliyar kasa guda.

Sai dai Janar Babangida ya ce hakan ba zai tabbata ba sai an samu hadin kan ’yan kasa musamman matasa, inda ya bukaci kowa ya kara himma.

Ya yi kira ga matasa a kan kada su bari ’yan siyasa su ribaci kuruciyarsu wajen amfani da su a matsayin karnukan zabe yayin da Babban Zaben kasar ya gabato.

Ya yaba wa kokarin gwamnatoci daban-daban a Najeriya wajen ganin kasar ta ci gaba da zama dunkulalliya, ya kuma yi kira don samun karin nasarori.

Ya ce burinsa shi ne ya ga Najeriya ta zama kasa mai karfi da yalwar arziki da hadin kai ta yadda zaman lafiya zai zarce komai.

Ya kuma bayyana fatansa na ganin cewa nan ba da jimawa ba za a warware tankiyar da ke tsakanin Gwamnatin Tarayya da Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU).