✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babu ɗalibin da zai bar makaranta saboda rashin kuɗi a mulkina – Tinubu

Ya ce duk dalibi mai karamin karfi zai samu rance, sai ya fara aiki ya biya

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, ya lashi takobin cewa a mulkinsa, babu ɗalibin da zai bar makaranta bai kammala ba saboda kawai ba zai iya biyan kudin makaranta ba.

Ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a bikin yaye dalibai karo na 33 da Jami’ar Fasaha ta Tarayya da ke Akure a Jihar Ondo ta shirya ranar Asabar.

Tinubu, wanda tsohon shugaban Kwalejin Lafiya ta Afirka ta Yamma, Farfesa King-David Terna Yawe, ya wakilta, ya bukaci kungiyoyi daban-daban na manyan makarantu da su hada kai da gwamnati domin tabbatar da zaman lafiya a cikin makarantun.

 Game da shirin gwamnatinsa na ba ɗalibai rance kuwa, Tinubu ya ce, “Wannan shiri zai ba dukkan dalibai masu karamin karfi damar karbar bashi mara ruwa, wanda za su iya biya daga baya, idan suka fara aiki.

“Matukar ina mulki, kamar yadda na fada a kundin manufofina, babu wani dalibi da zai bar makaranta saboda rashin kuɗi.

“Gwamnatina ba za ta yi wasa da nauyin da ya rataya a wuyanta ba a wannan bangaren. Za mu tabbatar dukkan manyan makarantu sun sami kudadensu saboda su yi ayyukansu yadda ya kamata,” in ji Tinubu.

Sai dai Shugaban ya shawarci kungiyoyin ma’aikatan manyan makarantu da su rungumi hanyoyin tattaunawa na ruwan sanyi a maimakon a kodayaushe su rika tsunduma yajin aiki, matakin da ya ce yana gurgunta tsarin ilimi a kasar nan.