✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babiana ’yar Tiktok ta yi auren ‘Wuf’

Sai ranar daurin aure amaryar ta wallafa hotuna da bidiyonsu ita da angon nata.

A ranar Asabar ne fitacciyar ’yar Tiktok Babiana Queen of Update ta amarce da angonta Muhammad Ezinwa.

Auren na Babiana dai ya jawo kace-nace a soshiyal midiya, inda wasu ke ganin bai kamata ba, saboda ta yi ‘Wuf’ da wanda a ganinsu ya yi mata yarinta.

Aure dai ya zo a ba-zata, domin sai ranar daurin auren ne amaryar ta wallafa hotuna da bidiyonsu ita da angon nata.

Bidyon farko da ta yi wa take da Amaryar Baby, ta dora shi ne ranar Asabar, kuma a ciki an ganta ta caba kwalliya tana rawa tana yi wa kanta liki da bandir din Naira dari biyar-biyar.

Na biyu kuma ta dora shi ne ranar Lahadi, wanda a ciki ita da angon suke rike da juna, ita kuma tana rawa. Wannan bidiyon dai ta yi masa suna da Mr and Mrs Eze.

Sai na 3 da na 4 kuma da ta sanya su ranar Litinin, inda ta yi godiya ga masu yi mata fatan alheri.

Guda daga cikin aminan amaryar, G-Fresh Al’amin, ya ce shagalin biki na tafe a gaba, a yanzu daurin aure aka fara.

Fitattun Jaruman Kannywood da ’yan Tiktok irinsu Rashida Mai Sa’a, Aisha Humaira, Aisha Najamu, da Mufida Adnan da aka fi sani da Moofy, da aminin Babianan G-Fresh taya ta murna ba.

Aminin amaryar dai G- Fresh ya taya ta murnan tare da yin nasiha ga wasu daga cikin abokansa na Kannywood da Tiktok kan muhimmacin aure.

Mu ma dai a nan muna fatan Allah Ya ba da zaman lafiya, Ya kuma kawo kazantar daki.