Kasuwannin da suka kasance a zamanin Jahiliyya kuma mutane suka ci gaba da kasuwanci da su a Musulunci:
550. An karbo daga Aliyu dan Abdullahi ya ce: “Sufiyan ya ba mu labari daga Amru daga dan Abbas (Allah Ya yarda da su), ya ce: “Ukkazu da Majanat da Zul-Majaz kasuwanni ne a Jahiliyya. Lokacin da Musulunci ya zo sai (Musulmi) suka rika ganin kamar sun yi sabo idan suka ci gaba da kasuwanci a cikinsu. Sai Allah Ya saukar da cewa: “Babu laifi a kanku idan (kuka yi kasuwanci) a lokutan ayyukan Hajji. (k:2:198).” Da kamar wannan dan Abbas ya fassara ma’anar ayar.
Babi na Talatin da Bakwai:
Kasuwancin rakumi mai kazuwa (kirci) ko mai ciwon kishirwa:
551. An karbo daga Aliyu dan Abdullahi ya ce: “Sufiyan ya ba mu labari ya ce, Amru ya ce, “A garin Makka ya kasance da wani mutum sunansa Nawwas kuma ya kasance da wani rakumi a gare shi, sai dan Umar (Allah Ya yarda da su), ya tafi domin ya sayi wancan rakumi daga abokin shi (Nawwas) sai abokinsa ya tafi gare shi ya ce: “Mun sayar da wannan rakumi,” sai ya ce, ga wa kuka sayar da rakumin? Ya ce “Mun sayar ga wani tsoho mai kama kaza da kaza,” sai ya ce, “Kaiconka! Wallahi dan Umar ne wannan.” Sai ya tafi gare shi (dan Umar) ya ce: “Hakika wani abokina ya sayar maka da wani rakumi mai cutar kishirwa, amma bai san kai ne, (ya sayarwa) ba.” Sai (dan Umar) ya ce, “Tafi ka kora ta (tafi da ita),” ya ce, “Lokacin da ya tafi domin ya tafi da ita: Sai (dan Umar) ya ce, “Bar ta, mun yarda da hukuncin Manzon Allah (SAW) cewa: “Babu zalunci a kasuwanci.”
Babi na Talatin da Takwas:
Sayar da makami lokacin fitina da waninta. Imran dan Husain ya karhanta (ki) cinikinsa a lokacin fitina:
552. An karbo daga Abdullahi dan Maslamata ya ce: “Daga Yahya dan Sa’id daga Umar dan Kasir ya ce, daga Abu Muhammad bawan Abu kattada daga Abu kattada (Allah Ya yarda da shi), ya ce, “Mun fita tare da Manzon Allah (SAW) a shekarar Hunain (Annabi ya ba ni taguwar sulke) sai na sayar da taguwar na sayi gona a yankin kabilar Bani Salmata, kuma lallai shi ne farkon dukiyar da na mallaka tunda na shiga Musulunci.”
Babi na Talatin da Tara:
Labarin mai sayar da turare da cinikin turaren Miski:
553. An karbo daga Musa dan Isma’il ya ce: “Abdulwahid ya ba mu labari ya ce, Abu Burdata dan Abdullahi ya ba mu labari ya ce, “Na ji Abu Burdata dan Abu Musa ya ce, daga Babansa (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce, “Misalin mazaunin (wurin zaman) kwarai da mazauni sharri (mummuna). Kamar misalin mai sayar da turare da makerin bakin karfe ne, babu abin da mai sayar da turare zai dame ka face kodai ka saya ko ka samu jin kanshi. Amma makeri zai kona maka gida ko tufafi ko ka ji mummunan wari.”
Babi na Talatin da Shida:
Kasuwannin da suka kasance a zamanin Jahiliyya kuma mutane suka ci gaba da kasuwanci da su a Musulunci:550. An karbo daga Aliyu dan Abdullahi ya…