Babi na Bakwai: Idan mutum ya yi kyautar wani abu ga wakili ko mai fansar jama’a ya halatta. Bisa fadin Annabi (SAW) ga kabilar Hawazini lokacin da suka roke shi ganimomi. Sai Annabi (SAW) ya ce: “Na ba ku rabona.”:
43. An karbo daga Sa’ad dan Ufair ya ce: “Laisu ya ba mu labari ya ce, Ukail ya ba ni labari daga dan Shihab ya ce: “Urwata ya ambata cewa, lallai Marwan dan Hakam da Miswar dan Makhramata sun ba shi labari cewa: “Lallai Manzon Allah (SAW) ya mike lokacin da tawagar Hawazin suka zo masa suna masu mika wuya (Musulmi). Sai suka roke shi da ya mayar musu da dukiyarsu da fursunan yakinsu. Sai Manzon Allah (SAW) ya ce, musu fiyayyen magana gare ni wanda ya fi gaskiya. Ku zabi daya cikin abubuwa biyun nan da kuka ambata. Ko dai fursunan yaki, ko kuma dukiya don haka zan jinkirta rabonsu ga jama’a. Manzon Allah (SAW) ya saurara musu don su zabi daya, har fiye da kwana goma lokacin da ya komo daga da’ifa. Lokacin da ya bayyana musu cewa, lallai Manzon Allah (SAW) ba zai mayar musu duka biyu face daya cikin abubuwa nan biyu, sai suka ce, “Lallai mun zabi fursunan yakinmu.” Sai Manzon Allah (SAW) ya mike ya yi wa Allah yabo da abin da ya dace da Shi, sa’an nan ya ce: “Bayan haka, lallai wadannan ’yan uwanku sun zo mana suna masu tuba, kuma lallai ni, na ga ya kamata in mayar musu da fursunan yakinsu. Wanda ya so ya ji dadi da haka, to, ya aikata, wanda kuma yake son rabonsa sai mu ba shi shi daga abin da Allah Ya ba mu na ribar yaki sai ya aikata. Sai mutane suka ce, “Lallai mu bayar da su ga Manzon Allah (SAW). Sai Manzon Allah (SAW) ya ce, “Lallai mu, ba mu sani ba, ko da wanda zai yi muku izini cikin wannan ko da wanda ba zai yi muku izini ba, ku koma ku yi shawari har ku aiko mana masanan al’amuranku (shugabanninku) gare mu. Sai mutane suka koma masanan al’amuransu suka yi magana da su, sa’an nan suka komo zuwa ga Manzon Allah (SAW) suka ba shi labarin cewa: “Lallai su, sun bayar da rabonsu kuma sun yi izini.”
Babi na Takwas: Wanda ya wakilta wani ya yi kyauta amma bai bayyana ko nawa ne yake so a ba da kyautar ba, sai wanda aka wakilta ya yi kyauta da abin da mutane suka sani (alheri):
44. An karbo daga Almakkiyyu dan Ibrahim ya ce: “dan Juraij ya ba mu labari daga Adda’u dan Abu Rabah da waninsa, sashinsu na kari bisa maganar sashi cewa, ba kowane mutum ne ya iske dukkansu ba, daga Jabir dan Abdullahi (Allah Ya yarda da shi) ya ce, “Mun kasance tare da Annabi (SAW) a cikin wata tafiya, sai na kasance bisa wani rakumi mai nauyin tafiya (mara sauri) wanda ya kasance a karshen (bayan) jama’a. Sai Annabi (SAW) ya shude da ni bisa hanya, sai ya ce: “Wane ne wannan? Na ce, “Jabiru dan Abdullahi ne. Ya ce, “Me ya faru? Na ce, “Na kasance bisa wani rakumi mara sauri.” Ya ce, “Shin kana da wata danyar bulala? Na ce, “Na’am.,” Ya ce, “Ba ni shi.” Sai na ba ita, sai ya buge shi ya yi masa tsawa, sai ya kasance gaba ga jama’a. (Annabi) ya ce, “Ka sayar mini da shi.” Sai na ce, “Na kane (na bar maka) ya Manzon Allah! Ya ce, “Ka sayar mini da kudina, na saye shi bisa Dinari hudu, amma kai za ka haushi har zuwa Madina. Lokacin da muka kusanci Madina sai na kasance ina tafiya ta bangaren gidana, sai (Annabi) ya ce, “Ina kake son tafiya? Na ce, “Na yi aure da wata mace wadda na jima ba ta tare da kowa tare da ita. Sai (Annabi) ya ce, “(Budurwa ko bazawara. Na ce: Bazawara ce.” Ya ce: Ina da dai budurwa ka aura, wadda za ka yi wasa da ita, kuma za ta yi wasa da kai? Na ce, “Lallai Babana ya mutu ya bar ni da kanne mata don haka na yi nufin in auri macen da za ta lura da su idan ba ni gida. Ya ce, “Madalla.” Lokacin da muka isa Madina ya ce, “Ya Bilal ka biya shi kuma ka kara masa, sai ya ba shi Dinari hudu ya kara masa da kiradi. Jabir ya ce, “karin Manzon Allah (SAW) ba ta rabuwa da ni, kuma kiradin nan bai rabuwa da Jabir dan Abdullahi.” (Abin da wannan Hadisi ya koyar shi ne Bilal ya bayar da kiradi daya ga Jabir, saboda Annabi (SAW) bai amabci yawan abin da zai kara masa ba).