A yayin da bukukuwan Babbar Sallah ke karatowa, matafiya na kokawa kan yadda farashin tikitin jirgin sama ya yi tashin gwaron zabo a Najeriya.
Tsadar tikitin ta fi shafar matafiya masu zuwa yankin Arewa, inda kudin tikitin Legas zuwa Yola babu dawowa a Max Air ya kai N135,000, Legas zuwa Sakkwato kuma N128,000.
- An kama Kwamandan NSCDC kan damfarar masu sayen filaye a Abuja
- NAJERIYA A YAU: Ayyuka Na Musamman A Kwanaki 10 na Farkon Watan Dhul-Hijja
Kudin tikitin tafiya falle daya daga Legas zuwa Kano ko Maiduguri ya kai N105,000 a jiragen Azman da Max Air da Air Peace sabanin N70,000 da suke karba a kwanakin baya.
Azman na karbar N99,749 falle daya daga Legas zuwa Kaduna, Arik kuma N122,196 daga Legas zuwa Sakkwato, Legas zuwa Yola kuma tsakanin 101,205 zuwa 122,196, gwargwadon lokacin da mutum ya sayi tikitin.
Legas zuwa Ilori a Air Peace ya tashi daga N50,000 zuwa N70,000; Abuja zuwa Katsina ko Kano a Max Air N75,000.
Matafiya dai na kokawa kan tsadar tikitin, amma kamfanonin zirga-zirgar jiragen sama sun dora laifin a kan tsadar man jirgi.
“Ka san yanzu kudin litar man jirgi ya haura N700? To yaya za mu yi?
“Kokari muke yi mu sa farashin da ba za mu karye ba,” inji Shehu Wadda, Babban Daraktan Kamfanin Max Air.
Wani mai sharhi kan sufurin jiragen sama, Babatunde Adeniji, ya shaida wa wakilinmu cewa ba farashin tikitin jirgi ba ne kawai ya tashi a Najeriya.
Ya ce, “Shin kudin tikitin jirgi ne kawai ya karu? Ai ba yadda za a yi hakan ta faru idan babu dalili? To ya ake so kamfanonin zirga-zirgar jiragen sama su yi?
“Tabbas ba za a rasa rangwame ba, amma babu makawa a samu karin farashi muddin kudin abubuwan da ake amfani da su suka ci gaba da karuwa yadda ake gani yanzu”.
A ranar Asabar 9 ga watan Yuli, 2022 ne dai al’ummar Musulmi a Najeriya za su yi Babbar Sallah.