Gwamnatin Jihar Kano ta wa daliban makaranta na Jihar hutun mako daya don yin bikin Babbar Sallah.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Kwamishinan Ilimi na Jihar, Malam Muhammad Sanusi Sa’id Kiru a ranar Alhamis.
- ’Yan bindiga sun kashe Janar din soja, sun sace matarsa
- Gwamnati ta ayyana hutun Babbar Sallah a Najeriya
Sanarwar ta ce dalibai za su yi hutun mako dayan ne wanda zai fara daga ranar 18 zuwa 25 ga Yulin 2021.
Kazalika, sanarwar ta umarci iyayen yara musamman wadanda suke a makarantun kwana da su kwaso ’ya’yansu a ranar Asabar mai zuwa.
Sai dai sanarwar ta ce hutun bai shafi daliban da ke zana jarabawar kamma sakandire ta NECO ba.
Har wa yau, Kwamishinan ya ce gwamnatin Jihar ta tanadi shirye-shirye da zasu farantawa daliban rai a yayin bukukuwan sallah.