Babban mai shiga tsakani a rikicin Falasdinawa da Isra’ila, Saeb Erekat ya rasu yana da shekaru 65 a duniya.
Saeb, wanda aka yi wa dashen koda a shekarar 2017 a kasar Amurka dai ya kamu da cutar COVID-19 a farkon watan Oktoban 2020, kamar yadda ofishin masu shiga tsakani na Falasdinawa ya tabbatar.
- Falasdinu ta janye daga kungiyar kasashen Larabawa
- Ba za mu kara amincewa da Amurka ba – Shugaban Falasdin
Daga bisani dai an kai shi Asibitin Hadassah dake birnin Kudus a cikin wani matsanancin yanayi ranar 18 ga watan Oktoba.
Saeb dai na daya daga cikin fitattun ‘yan siyasa dake kan gaba Falasdinu a ‘yan shekarun da suka wuce wajen tattaunawa da hukumomin Isra’ila tun kusan shekarun 1990.
Ya taba zama mataimakin shugaban ayarin Falasdinawa zuwa taron birnin Madrid na kasar Spain a shekarar 1991, lokacin da gwamnatin shugaban Amurka George Bush ke fafutukar lalubo bakin zaren rikicin kasar da Isra’ila.
Marigayi Saeb dai ya sami girmamawa daga Yahudawan Isra’ila da dama wadanda ya sha zama a teburin tattaunawa da su a baya, ciki har da tsohon jami’in huldar diflomasiyyar kasar, Alon Pinkas.