✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Babban Limamin Abeokuta ya kwanta dama

Babban limamin lardin Egba a jihar Ogun, Sheik Liadi Orunsolu ya riga mu gidan gaskiya. Allah Ya yi wa Sheik Orunsolu rasuwa ne a gidansa…

Babban limamin lardin Egba a jihar Ogun, Sheik Liadi Orunsolu ya riga mu gidan gaskiya.

Allah Ya yi wa Sheik Orunsolu rasuwa ne a gidansa da ke Abeokuta da sanyin safiyar Talata, 26 ga watan Mayu bayan ya dade yana fama da rashin lafiya da ke da alaka da tsufa ko yawan shekaru.

A lokacikin rayuwarsa, Sheik Liadi Orunsolu shi ne jagorantar lardin ya da ya hadar da Birnin Abeokuta da wasu sassan jihar.

Aminiya ta gano cewa Shehun malamin ya kwanta jinya a wannan karon tun gabanin watan azumin Ramadan.

Za kuma a yi masa sutura, a binne shi da misalin karfe 4 na yamma a ranar Talatar bisa tsarin addinin Islama.