Tshohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ya ce tarin bashin da ake ciyowa ’ya’ya da jikoki ba karamin laifi ba ne.
Obasanjo na tsokaci ne kan yunkurin Gwamnatin Tarayya na sake ciyo sabon bashi.
- Babu barazanar da za a yi mana kan ci gaba da mulki a 2023 – Dattawan Arewa
- Kin janye yajin aikin likitoci raini ne ga kotu – Ngige
A makon da ya gabata, Shugaban Kasa Muhamamadu Buhari ya aike wa da Majalisar Dattawa bukatar neman amincewarta don ciyo sabon bashin $4,054,476,863 da kuma €710 domin cike gurbin kashe kudade na 2018 zuwa 2020.
A tattaunarwasa da gidan Talabijin na Channels, Obasanjo muddin aka ci gabo da karbo basukan ba tare da la’akari da hanyoyin biyansu ba, to za su iya zama karfen kafa ga gwamnatoci masu zuwa.
Ya ce ko da yake ciyo basukan ba illa ba ne, amma ya zama wajibi a rika la’akari da yadda za a biya su.
“Iadn misali zaka gina gida, sai ka aro rabin kudin kai kuma kana da rabi, ka ga kenan zaka biya rabin, ina tunanin babu wata illa. Amma ida ya kasance sai ka aro kudi zaka iya ciyar da kanka da iyalanka, ina ganin akwai wauta a ciki.
“Ciyo bashi tare da tara shi ga ’ya’ya da jikoki babban laifi ne. don me za a aro kudaden?
“Idan kana cin bashi don kashe kudaden gwamnati na yau da kullum akwai shirme a ciki. Idan kuma don ayyukan da za su biya kansu ne, wannan babu matsala. Sannan tsawon wanne lokaci za a dauka kafin a iya biya?,” inji Obasanjo.
Tsohon Shugaban Kasar ya kuma ce zamanin mulkinsa tsakanin 1999 zuwa 2007 kasar na kashe Dala biliyan 3.5 wajen biyan bashi.
“Lokacin da na zo gwamnati a matsayin zababben Shugaban Kasa, mu kan kashe $3.5bn wajen biyan bashi, amma duk da haka basukan ba sa raguwa.”