✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Manyan jami’an kiwon lafiya sun kamu da Coronavirus a Badun

Babban Daraktan Asibitin Koyarwa na Jami’ar Badun, Farfesa Jesse Abiodun Otegbayo, ya kamu da cutar Coronavirus. A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na…

Babban Daraktan Asibitin Koyarwa na Jami’ar Badun, Farfesa Jesse Abiodun Otegbayo, ya kamu da cutar Coronavirus.

A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Twitter @UchCmd, babban jami’in ya bayyana cewa Asibitin Koyarwa ya shirya taron kwanaki biyar na musamman a kan cutar ta Coronavirus wanda aka fara ranar Litinin, amma ranar Laraba daya daga cikin mahalarta ya nuna alamun kamuwa, don haka aka dakatar da taron.

“Ranar Juma’a da safe sakamakon gwajin [da aka yi] ya nuna mutumin yana dauke da cutar saboda haka dukkan mahalrta taron (ciki har da ni) muka killace kanmu nan take yayin da aka dauki jininmu aka tafi a yi gwaji”, inji Farfesa Otegbayo.

Ya kara da cewa, “Abin bakin ciki, ranar Asabar da rana sakamakon ya fito ya kuma nuna cewa na kamu duk da ban nuna alamun kamuwa ba, kuma ina ci gaba da killace kaina”.

Bugu da kari, Shugabar Tsangayar Horar da Likitoci ta Jami’ar, Farfesa Olubunmi Olopade-Olaopa, da Mataimakinta, Farfesa Obafunke Denloye, su ma sun kamu.

Su ma sun bayar da sanrwar kamuwar tasu ne a wasu sakwanni da suka fitar a lokuta daban-daban.

Sanarwar kamuwar Farfesa Otegbayo da abokan aikinsa ta zo ne sa’o’i kadan bayan kamuwar gwamnan Jihar Kaduna Nasiru El-Rufa’i da shugaban hukumar kula da shige da fice ta Najeriya Muhammad Babandede.