✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babban basaraken Jihar Oyo, Olubadan na Ibadan, ya rasu

Ya rasu da sanyin safiyar Lahadi yana da shekara 93.

Babban basaraken Jihar Oyo, wato Olubadan na Ibadan, Oba Saliu Adetunji, ya rasu.

Wata majiya daga fadar ta Olubadan da ta nemi a sakaya sunanta ta shaida wa wakilinmu cewa basaraken ya rasu ne da sanyin safiyar Lahadi a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ibadan.

Ya rasu yana da shekara 93 a duniya.

Aminiya ta gano cewa basaraken mai daraja ta daya ya sha fama da jinya sakamakon rashin lafiya a ’yan makonnin da suka gabata.

“Ko da yake har yanzu ban karasa fadar ba, amma na ji labarin cewa ya rasu ne a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ibadan da safiyar Lahadi. Zan ba ka cikakken bayani da zarar na karasa fadar,” inji majiyar.

Marigayin dai ya dare karagar ta Olubadan ne a ranar hudu ga watan Maris na shekarar 2017.