✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babban Bankin Lebanon ya dakatar da biyan tallafin man fetur

Babban bankin kasar Lebanon ya wajabta amfani da farashin canjin Dala da ya sanya, yayin da kasar ke ci gaba da fuskantar matsalar tattalin arziki.

Babban bankin kasar Lebanon ya wajabta amfani da farashin canjin Dala da ya sanya, yayin da kasar ke ci gaba da fuskantar matsalar tattalin arziki.

A shekarar da ta gabata, babban bankin ya ce zai karya farashinsa na canjin Dalar Amurka da kuma iya adadin Dala da zai bayar, sakamakon raguwar ajiyar kudaden kasashen waje.

Sai dai kuma bai aiwatar da hakan ba a kan kudin kasar a shafinsa na canji na Sayrafa.

Amma a makonnin baya-bayan nan, an rage yawan Dala da ake bayarwa ta hanyar Sayrafa, a hankali, a matsayin wani babban shiri na kawo karshen tallafin da gwamnatin kasar ke bayarwa a kan mafi yawan kayayyaki, sakamakon durkushewar tattalin arziki da kasar ta shekara hudu a ciki.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito Kakakin babban bankin kasar yana fada a ranar Litinin cewa, a yanzu masu shigo da kaya za su rika samun canjin Dala daga kasuwar bayan fage.

Kasuwannin canjin kudi na bayan fage a Lebanon na bayar da Dala a kan kimanin Fam 35,000 na kudin kasar.

Farashin canjin a Sayrafa a makon da ya gabata ya kai kimanin Fam 28,000 na kudin Lebanon.

Wani mamba na kungiyar kamfanoni masu shigo da man fetur, Maroun Chammas, ya ce “Idan aka samu karin sauyi a canjin kudi, to za a samu raguwar farashin man fetur.”

Farashin lita 20 na man fetur a Lebanon ya yi tashin gwauron zabo da fam 20,000 a ranar Litinin, idan aka kwatanta da sauyin yau da kullun na wasu ’yan Fam dubu a cikin makonnin da suka gabata.