Shugaban Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS), Muhammad Babandede ya ajiye aiki bayan shafe shekara 36 yana aiki.
A yanzu dai Mataimakin Shugaban Hukumar mai kula da bangaren kudi, Idris Isah Jere ne zai rike hukumar har zuwa lokacin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai nada sabon shugaba.
An nada Babandede ne a shugabancin hukumar a shekarar 2015 inda ya karbeta daga hannun Martin Kure Abeshi.
Ya kawo sauye-sauye da dama a hukumar da suka hada da mayar da Fasfo din Najeriya zuwa na zamani, saukaka hanyoyin bayar da shi da kuma bullo da shirin bayar da biza bayan shigowa kasa.
Da yake jawabi yayin wani taron ban-kwana da aka shirya don karrama shi ranar Juma’a, Babandede ya ce ya bar hukumar fiye da yadda ya sameta.
Ya kuma yaba wa ma’aikatanta, wadanda ya ce ya sami nasarorin ne sakamakon hadin kansu, inda ya yi kira ga wanda zai gaje shi da kada ya yi watsi da su.
Babandede ya kuma yi alkawarin cewa zai ci gaba da kasancewa jakadan hukumar tare da alkawarin bayar da gudummawa a duk lokacin da aka bukaci hakan.
Ya dai shafe shekara biyar da wata hudu a matsayin shugaban hukumar ta NIS.