Jarumin barkwanci da ke fitowa a matsayin Bayarabe, Baban Ramota ya ƙalubalanci masu shirya finafinan Kannywood da su riƙa tuntuɓar masana wurin samar da finafinansu.
Muhammad Aƙilu, wanda aka fi sani da Baban Ramota ko Baban Mulika ya bayyana haka ne a hirar da ya yi da Aminiya.
Ya ce masu shirya finafinai na da sun nemin ilimin abun yayin da na yanzu ke aiki da ka.