Shin talakawan Najeriya za su jure salon mulkin Buhari kuwa? Wannan ita ce tambayar da kan bijiro mini a duk sa’adda na yi nazarin halin da al’ummar Najeriya ke ciki hakikanin gaskiya mafi yawan talakawan Najeriya sun zabi sabuwar gwamnati ne saboda kyakkyawan zaton samun afuwar talaucin da azzaluman kasar nan suka jefa mu, musamman ta inda za ka ga mutum daya ya kwashe dukiyar da miliyoyin mutane za su anfana.
Hakikanin gaskiya za mu iya cewa, kwalliya ta fara biyan kudin sabulu saboda yadda asirin wasu azzaluman ya fara tonuwa, musamman bankade-bankaden da a ka fara a kan badakalar kudin sayen makamai, domin magance matsalar tsaro, amma abin takaici sai ga shi an yi watanda da kudin, ta inda aka dinga rarraba kudin hakan yasa aka fita batun sayan makamai badan komai ba sai dan saboda kisan da ake yi ba ya shafarsu; yana shafar talakawa ne kawai. Ta nan wajen za mu iya cewa, an fara samun nasara, amma wani abu da yanzu yake daukar hankalin mutanen Najeriya, shi ne, sabon salon da gwamnatin tarayya ta dauka a kan tattalin arzikin kasa, musamman yadda aka hana bai wa masu sana’ar Canjin kudaden kasashen waje Dalar Amurka. Abin tambaya, ko hakan zai shafi talakawan Najeriya? ni dai a irin tunanina indai har za a hana bai wa mutanen Najeriya isassun kudin Dala domin yin safara da su wajen sayo kaya a kasashen ketare a wannan lokacin, to akwai gagarumin kuskure. Domin kuwa a watanni kadan da fara mulkin Buhari ba a dauki hanyar dawo da masana’antunmu da ke cikin gida ba.
Ya kamata gwamnati ta fara gyara cikin gida, wato dawo da martabar masana’antunmu, ta hanyar inganta wutar lantarki, tunda ta haka ne kawai kwalliya za ta biya kudin sabulu, musamman a wannan lokaci da talaka ya fara kosawa.
Baka Noma ya rubuto makalarsa ne daga Sani Mainagge Kano 08069735151.
Baba Buhari Talakawa sun fara kosawa
Shin talakawan Najeriya za su jure salon mulkin Buhari kuwa? Wannan ita ce tambayar da kan bijiro mini a duk sa’adda na yi nazarin halin…