✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba’amurken kasar Sin ya kera jirgin da ke sauka a garejin gidansa

A Jihar Chicago ta kasar Amurka an samu jama’a da injiniyoyi da suka mayar da bayan gidansu filin jiragen sama, har ma suna ajiye kananan…

A Jihar Chicago ta kasar Amurka an samu jama’a da injiniyoyi da suka mayar da bayan gidansu filin jiragen sama, har ma suna ajiye kananan jirage a garejinsu. Daga cikin wadannan injiniyoyi akwai wani mutumin kasar Sin zaunannen Amurka, mai suna Dabid Hu, wanda injiniya ne da ke aiki a kamfanin kayan lantarki na Nokia.
Wannan Ba’amurken dan kasar Sin ya fara kera karamin jirgin sama ne tun a shekarar 2006. Wato shekara 10 ke nan da ya fara wannan aiki daga zane-zane a kwali, har ya fara sayen sassan jirgin inda ya rika harhadawa. Dabid dai ya hada jirginsa shi kadai, inda ya yi amfani da lokutan da ba ya yin aikin komai.
Jirgin Dabid Hu yana da nauyin kilo 590, sannan yana gudun kilomita 290 a kowace sa’a. Don haka yana iya karade nisan kilomita 644 zuwa 724 a lokaci kankane.
Bayan da hukumar kula da jiragen sama ta Amurka ta tantance ingancin jirgin, sai ya fara tashi a cikin watan Yunin bana.
“Na sha tuka jiragen sama a tsawon rayuwata, amma wannan shi ne karamin jirgi mafi inganci da na taba tukawa. A tsarin sarrafa injinsa yana da matukar nagarta ga dadin sauti,” a cewar Musgrabe, wani jami’in bayar da horo a kamfanin hada-hadar jiragen sama na Blue Sky Aero Inc., kamar yadda ya sanar da kamfanin Dillancin Labarai na dinhua.
Ya ce karamin jirgin yana da “cikakkiyar kariya,” inda ya kara da cewa, “komai a cikin jirgin yana da cikakkiyar shaidar amincewata.”
Tun a watan Yunin bana aka fara hada-hadar tashi da wannan jirgin saman, inda a halin yanzu ya yi tafiye-tafiye na wata biyu, kuma ya shafe sa’o’i 32, ta yadda aka kiyasta a kowane mako yana cin dogon zango da yakan shafe akalla sa’o’i biyu zuwa uku. Kuma babu wata matsala da ta auku a gare shi.
“Wannan aiki ne da aka shafe shekara 10 ana gudanar da shi. Iyalina sun fuskanci dimbin kalubale wajen tallafa mini, inda suka fuskanci damuwa da matsin rayuwa da rashin kudi. Tamkar dai kowane gagarumin aiki, amma dai farin cikina mun kai ga gaci,” a cewar Hu, bayan da ya tashi da jirginsa a filin jirgin saman Morris da ke bayan gidansa a ranar Lahadin da ta wuce. “Na dai tashi sama a wannan jirgin. Don haka na bude babin sabuwar rayuwa, inda kuma nake hangen tunkarar wani al’amari nan gaba,” inji shi.