✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba zan zaba wa majalisa shugabanni ba – Buhari

Zababben Shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari ya ce ba zai tsoma baki cikin batun zaben shugabannin Majalisar Dokoki ta kasa ba. Janar Buhari ya ce,…

Zababben Shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari ya ce ba zai tsoma baki cikin batun zaben shugabannin Majalisar Dokoki ta kasa ba.

Janar Buhari ya ce, “Akwai tsarin zaben shugabannin Majalisar Dokoki ta kasa, kuma ba zan tsoma musu baki a cikin lamarin zaben shugabanninsu ba.”
Ya yi watsi da labaran da wasu kafafen watsa labarai suka bayar cewa yana goyon bayan wani dan takara. “Ina shirye don in yi aiki da shugabannin da Majalisar Dattawa ko ta Wakilai suka zaba,” inji Buhari a wata sanarwa da ofishin labaransa ya fitar a shekarajiya Laraba.
“Ban damu wane ne mutumin ba ko daga inda ya fito ba,” inji sanarwar dauke da sanya hannun Kakakin Buhari Malam Garba Shehu.
Ya ce bai da wani bangare da ya zaba, kuma a shirye yake ya yi aiki da duk wani shugaban majalisa ba tare da lura daga wane yanki na kasar nan ya fito ba.
Janar Buhari ya ce shaci-fadin da kafafen watsa labarai da jama’a ke yi ya ginu ne bisa lura da abubuwan da suka faru a baya, inda ya tunatar da ’yan Najeriya cewa da gaske “CANJI” ya zo. Ya kara da cewa ya kamata kafafen watsa labarai da jama’a su fara tuna cewa “kida ya canja.”
“A yanzu Najeriya ta shiga wani sabon mulki, gwamnatina ba za ta so maimaita kura-kuran da gwamnatocin da suka gabata ba.”
’Ya’yan Jam’iyyar APC ta Janar Buhari sun shiga fafatawa kan wadanda za su zama shugabannin majalisun dokokin biyu, inda suka kasa samar da matsaya kasa da mako uku a kaddamar da gwamnatin Buhari.
Tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar an ce ya nuna wa Buhari cewa a matsayinsa na zababben Shugaban kas bai kamata ya kawar da kai daga batun shiyyar wadanda za su zama shugabanin majalisun biyu ba.
Sai dai wata majiya ta ce Buhari bai da sha’awar tsoma baki a batun shiyya-shiyya inda ya fi son a kyale ’yan majalisa su zabi shugabanninsu.
Wata majiya ta ce a ranar Talata Buhari ya shaida wa shugabannin Jam’iyyar APC cewa a shirye yake ya yi aiki da duk wanda ya zama shugaban Majalisar Dattawa ko ta Wakilai.
A Majalisar Dattawa dai, shiyyar Arewa maso Gabas da Arewa ta Tsakiya suka ja dagar neman shugabancin majalisar, yayin da a Majalisar Wakilai ake fafatawa a tsakanin Yakubu Dogara daga Bauchi da Femi Gbajabiamila daga Legas.