Gwamna Aminu Bello Masari na Jihar Katsina, ya kawo karshen rade-radin da ke cewar zai sake tsayawa takarar wata kujerar siyasa a babban zaben kasa na 2023.
Masari ya bayyana hakan yayin gabatar da tattaunawar farko ta bude wata kungiyar Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa NAN.
Yayin tattaunawar bude kungiyar ta NAN Forum, Masari ya ce ba zai nemi wata kujerar siyasa ba yayin da wa’adin mulkinsa na biyu a matsayin gwamna zai kare a 2023.
Masari ya ce aniyar da ya sa a gaba a yanzu ita ce mara wa matasa baya domin cimma burace-buracensu na riko da madafan iko.
Masari ya ce, “ba zan tsaya takarar wata kujera ba a jam’iyyar APC ko kuma a gwamnati.
“Na rike mukamin Shugaban Majalisar Wakilai ta Tarayya saboda haka mai kuma zan sake komawa nay i a Majalisar.
“A jam’iyyar APC kuma, na taba rike mukamin Mataimakin Shugaban Jam’iyyar na Arewa, saboda ina dalilin komawa ta na tsaya takarar wata kujera a jam’iyyar.
“A jiha kuma, na kai har matakin Gwamna, saboda haka yanzu ina gani lokaci ya yi da za mu bai wa matasa dama su taka rawar gani a fagen jagoranci.
Ana iya tuna cewa, Masari ta rike mukamin Kwamishinan Ayyuka, Gida da Sufuri na Jihar Katsina a tsakanin shekarar 1991 zuwa 1993.
Haka kuma, ya rike mukamin Shugaban Majalisar Wakilai ta Tarayya daga shekarar 2003 zuwa 2007, sannan kuma mukamain Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC na Arewa a shekarar 2013 kafin lashe zaben gwamnan Jihar Katsina har sau biyu a shekarar 2015 da kuma 2019.