Tsohon Shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya sake jaddada cewa ba zai sake kasancewa dan wata jam’iyyar siyasa a kasar nan ba, sannan ya kara da cewa ba zai yi amai ya lashe ta hanyar komawa jam’iyyar PDP ba.
Obasanjo ya fadi haka ne a yayin da yake zantawa da manema labarai, jim kaɗan bayan sun kammala wata ganawar sirri da Shugaban Rikon kwarya na Jam’iyyar PDP kuma tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Alhaji Ahmed Maƙarfi a mahaifarsa Abeokuta ranar Talatar da ta gabata.
Tsohon shugaban kasan ya jaddada cewa ya tsame hannayensa daga duk wani abu da ya shafi siyasa, wanda kuma a cewarsa, “A jiya ni dan PDP ne, amma ba yanzu ba. Saboda ‘yan magana sun ce idan kare ya yi amai, to ba zai koma ya cinye aman ba. Amma wannan ba zai hana ni bayar da gudumawata wajen ciyar da Nijeriya gaba ba. Babu abin da Nijeriya ke buƙata fiye da samun jam’iyya mai karfi wacce za ta mulki ƙasar nan, tare kuma da samun jam’iyyar adawa mai tasiri, ta yadda za a samu cigaban dimokuraɗiyya a Najeriya.”
Ya ci gaba da cewa, “Na sha faɗin wannan, matukar ana so dimokuradiyyarmu ta bunkasa, to sai an samu jam’iyya mai ƙarfi wacce za ta rike ragamar gwamnati, sannan kuma a samu jam’iyyar adawa mai tasirin gaske. Dole hakan za a yi, idan kuma ba haka ba, jam’iyyar da ke rike da gwamnatin ce kawai za ta ci gaba da yin kidinta taa rawarta.”
Haka zalika da yake bayani game da ganawar sirrin da suka yi da shugaban PDP kuwa, tsohon shugaban ƙasan ya ce, wannan wata haɗuwa ce ta tsoffin aminai. Domin lokacin da yake shugaban ƙasan Najeriya, shi kuma Maƙarfi yana gwamnan Jihar Kaduna.
“Na sanar da Shugaban jam’iyyar ta PDP cewa ni tsohon ɗan jam’iyyar PDP ne a da, amma banda yanzu. Ba na ma fatan in sake komawa PDP. Shugaban jam’iyyar dai ya zo ya gaishe ni, ni ma kuma na gaishe shi. Don haka ku ‘yan jarida za ku iya tafiya don ku baiwa shugaban jam’iyya dama ya huta,” a cewar Obasanjo.