✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba zan saci dukiyar Najeriya ba-Buhari

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya umarci ‘ya’yansa su dage su yi karatu, domin ba zai saci dukiyar Najeriya ba.   A wani shiri na musamman…


Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya umarci ‘ya’yansa su dage su yi karatu, domin ba zai saci dukiyar Najeriya ba.

 

A wani shiri na musamman a kan Buhari, wanda Gidan Talabijin na Kasa wato NTA ta gabatar, Buhari ya ce yadda mutane ke kaunarsa ne ya sa yake siyasa. Sannan ya ce burinsa shi ne ya yi mulki mai kyau da aminci.

 

“Ina yin sallah sau biyar a rana domin in gode wa Allah da Ya sa mutane suke kaunata. Wannan abin murna ne yadda talakawa suke kaunata. Babban burina shi ne in yi shugabanci mai kyau da aminci a fili ba boye-boye."