✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba zan karbi kujerar da ba tawa ba —Shekarau

Na sanar da INEC cewa na janye takara.

Sanatan Kano ta Tsakiya, Malam Ibrahim Shekarau, ya fito fili ya bayyana matsayinsa na cewa ba zai taba karbar kujerar da bai neme ta ba.

Furucin tsohon gwamnan na Kano nan zuwa ne yayin da a ranar Litinin da ta gabata Hukumar Zabe ta Kasa INEC ta ayyana Shekarau a matsayin wanda ya lashe zaben kujerar Sanatan Kano ta Tsakiya a karkashin tutar jam’iyyar NNPP.

Sanarwar da INEC ta yi ta janyo rudani a tsakanin masu ruwa da tsaki, inda har wasu ke gunagunin cewa Sanata Shekarau zai iya karbar kujerar duk da bai takara ba.

Sai dai a cewar mai magana da yawun Shekarau, Dokta Sule Yau Sule, “Malam ba ya cikin jerin ‘yan takara don haka ba zai karbi abin da ba nasa ba ne.

Ya bayyana cewa, “tun kafin zabe ya rubuta wa INEC cewa ya fita daga takarar kujerar wanda kuma Hukumar Zaben ta samu takardar duk da cewar ba ta rubuto amsa ba.

“A wancan lokaci, jam’iyyar ce take da wannan alhaki kuma ya kamata ta cire sunan dan takara wanda kuma na san jam’iyyar ta yi.

“Kodayake a bisa tsari, kafin a yi zabe magana ce tsakanin INEC da jam’iyya, amma a yayin da aka yi zabe lamari ya kuma koma tsakanin dan takara da Hukumar INEC.”

Tun dai lokacin da Sanata Ibrahim Shekarau ya bayyana batun barin jam’iyyar NNPP wacce yake yi mata takarar Sanata a wancan lokaci, jam’iyyar ta NNPP ta maye gurbinsa da Rufa’i Sani Hanga.

Aminiya ta ruwaito cewa, tun a watan Agustan bara ya sauya sheka daga jam’iyyar NNPP zuwa PDP, bayan da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar ya yi zawarcinsa.