✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ba zan daina fada wa masu mulki gaskiya ba —Sarkin Musulmi

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya ce ba zai daina fada wa gwamnati gaskiya ba, duk da cewa wasu ‘yan siyasa…

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya ce ba zai daina fada wa gwamnati gaskiya ba, duk da cewa wasu ‘yan siyasa ba sa son hakan.

Sarkin ya fadi haka ne a jawabinsa a yayin taron tunawa da Dokta Abubakar Bukola Saraki karo na 10 wanda aka yi ranar Litinin a Abuja.

Taken taron shi ne “Tattauna wa kan shugabanni da mabiyasu” wanda Sarkin ya ce, taken ya dace, la’akari da muhimmnancinsa.

“Yanzu lokaci ne na siyasa, kuma lokacin da muke kokarin zabo wadanda za su ja ragamar kasar nan zuwa tudun mun tsira, ya kamata mu mayar da hankali, kar mu yi zaben tumun dare”.

“Kodayake idan muka fadi gaskiya, wasu shugabannin ba sa jin dadi, amma ba za mu daina ba, duk halin da ake ciki, ko su so, ko kar ka su so,” inji Sarki Musulmin.

Sarkin dai shi ne ya shugabanci taron a inda aka gayyato wasu fitattun mutane daga wajen kasar nan domin yin jawabi.

Taron ya samu halartar musu rike da mukaman siyasa da kuma manyan ma’aikatan gwamnati.

 

%d bloggers like this: