Tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya yi alkawarin yin iya kokarinsa wajen sauke nauyin da Gwaman Jihar Kaduna Nasiru El-Rufai ya dora masa.
Sanusi II wanda tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriyan (CBN) ne ya yi alkawarin ne a ganawarsa da El-Rufai a ziyarar aiki ta mako guda da ya fara a jihar ranar Lahadi.
Ziyarar da ya fara kaiwa ke nan tun bayan Gwamnatin Jihar Kano ta tube shi daga sarautar Kano da kuma komawarsa Legas da zama.
A tsawon ziyarar, zai gana da masu ruwa da tsaki na Jami’ar Jihar Kaduna (KASU) da Hukumar Zuba Jari ta jihar (KADIPA), a matsayin Uban Jami’ar da Mataimakin Shugaban Kwamitin Darektocin hukumar.
“Ina tabbatar maka cewa zan yi iya kokarina wajen taimaka wa ayyukanka na bunkasa jihar; Zan kuma bayar da gudunmuwa ga Jami’ar Jihar Kaduna yadda ya kamata.
“Duniya shaida ce a kan yadda ka mara bin baya a lokacin da nake matukar bukata. Na yi wa kaina alkawarin duk lokacin da na fita daga Legas to kai ne zan fara ziyarta in yi wa godiya.
Bayan Gwamna Abdullahi Ganduje ya tube Sanusi II a matsayin Sarkin Kano ne El-Rufai wanda yake sahun farko na kai masa ziyarar jaje, ya nada shi mukaman guda biyu.
A matsayin na Mataimakin Shugaban Kwamitin Darektocin karkashin jagorancin Hadiza Balarabe, Mataimakiyar Gwamnan Jihar, Sanusi zai rika yin taro da su a duk bayan wata uku.
A matsayin Uban Jami’a kuma, wanda sarakai aka fi nadawa, ana fatan karbuwarsa da kwarewarsa za su taimaka wajen kawo muhimman ci gaba da KASU.
— Babu masaka tsinke saboda murnar zuwan Sanusi II
Saukar jirginsa ke da wuya, manyan jami’an Gwamnatin Jihar Kaduna suka tarbe shi kafin wucewa zuwa gidan Gwamanin Jihar.
Dubban masoya da masu rike da sarauta daga Jihar Kano sun yi tururuwa a garin Kaduna domin tarbar sa cikin farin ciki.
An yi ta sanya wakokin yabon Sanusi, wanda kai tsaye fara zuwa domin godiya da kuma ganawa da abokinsa, Gwamna El-Rufai.
— Kusancin Sanusi II da El-Rufai
A ranar 9 ga watan Maris, 2020 Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje ya sauke Sanusi daga Sarautar Kano, wanda ya hau a ranar 8 ga Yuni, 2018 bayan rasuwar Sarkin Kano na 13, marigayi Alhaji Ado Bayero.
Bayan sauke shi bisa zargin rashin biyayya, an tsare Sanusi a Jihar Nasarawa kafin daga baya Kotun Daukaka Kara ta Tarayya ta yi ta ba da umarnin sakinsa.
Ba a jima ba, El-Rufai ya ba shi mukamai biyu a Gwamnatin Jihar Kaduna.
Gwamnan ya ziyarci Sanusi II bayan Ganduje ya sauke shi aka kuma tsare shi a Jihar Nasarawa, har suka yi sallar Juma’a tare a garin Awe.
Daga nan El-Rufai da Sanusi suka dawo Abuja tare, inda tsohon sarkin ya hau jirgi zuwa Legas, inda ya koma da zama.
Alhaji Aminu Ado Bayero shi ne ya maye gurbin Sanusi, wanda ya gaji Mahaifinsa, Sarki Ado Bayero da ya rasu bayan shekara fiye da 50 yana Sarkin Kano.