Ministan Harkokin ’Yan Sanda, Maigari Dongyadi, ya bayyana dalilin da ya sa Shugaba Buhari bai ziyarci iyalan matafiyan da ’yan bindiga suka yi wa kisan gilla a Jihar Sakkwato.
Dingyadi, ’yan ta’adda na yin kashe-kashe ne kusan ko’ina a fadin Najeriya, shi ya sa ba zai yiwu ga shugaban kasa ya ziyarci kowa ba, amma tura wakilai tamkar shugaban ne ya je da kansa.
- Yadda ’yan bindiga suka yi wa masu cin kasuwa kisan gilla a Filato
- Tsananin yunwa ya fara kashe yara a Afghanistan
“Wadannan hare-haren da ake kaiwa suna faruwa kusan a kullum, don haka ba zai yiwu a ce ya je ta’aziyya ko’ina ba, amma idan ya tura wakilai tamkar ya je da kansa ne,” a Dingyadi.
Ya bayyana haka ne a cikin wata tattaunawa da sashen Hausa na BBC, inda ya ce duba da yanayin aikin shugaban kasa, ba zai iya samun damar ziyara ga iyalan duk wadanda aka kashe ba.
Sai dai ya ce jami’an tsaro na aiki tukuru don ganin sun kawo karshen matsalar tsaro da ta addabi wasu yankuna na Najeriya.
Da yake mayar da martani, dan majalisar tarayya mai wakiltar yankin Sabon Birni, Aminu Boza, ya ce ba sa bukatar zuwan tawaga yankin nasu, abin da suke bukata shi ne a kawo karshen matsalar da suke ciki.
“Tabbas wakilan shugaban kasa sun ziyarce mu, amma ba shi ne abin da muke bukata ba. Abin da muke bukata shi ne daukar mataki.
“A karamar hukumata an kashe daruruwan mutane kuma har yanzu ba tare da daukar mataki daga Gwamnatin Tarayya ba, amma an kashe wani a Legas kuma an dauki mataki,” inji shi.
Aminiya ta rawaito yadda aka yi wa Buhari zanga-zanga a wasu sassan kasar nan, kan kisan da ’yan bindiga suka yi wa wasu akalla mutum 23 a yankin Sabon Birni da ke Jihar Sakkwato.
Halartar taron kaddamar da littafin jigo a jam’iyyar APC, Cif Bisi Akande, da shugaba Buhari ya yi, ya bar baya da kura inda mutane suka yi ta nuna bacin ransu kan bain da suka kira halin ko-in-kula da ya nuna.