Fatuhu Muhammad wanda yake dan wa ga Shugaba Kasa Muhammadu Buhari kuma dan Majalisar Wakilai ya ce bai ga ta zama a APC ba tun da aka zagi mahaifinsa.
Fatuhu dai shi ne yake wakiltar mazabar Daura, Sandamu da Mai’aduwa daga jihar Katsina, mazabar da Buharin ya fito.
- Wutar Kaikayi: Nazarin littafin Tarkon Mut’a (2)
- Kotu ta yanke hukuncin kisa ga Faston da ya kashe yaro ya binne gawar a coci
Dan Majalisar wanda ya sha kaye a zaben fid-da gwani da aka gudanar a jihar Katsina a kwanakin baya ya bayyana hakan ne lokacin da yake karin haske kan makasudin ficewarsa daga jam’iyyar.
Fatuhu ya fadi hakan ne a zantawarsa da sashen Hausa na BBC ke bayan saukar matakin.
Ya ce, kiran sunan mahaifinsa da tsagin da suka yi nasara a kansa yayin zaben fid-da gwanin suka yi gatse-gatse sannan suka kunduma masa zagi ne ya sa shi ficewa daga jam’iyyar.
Har wa yau ya kara da cewa dama tun da dadewa ya yi yunkurin ficewa amma saboda dakatar da shi da wasu daga cikin masu taimaka masa a sha’anin siyasa suka yi ya sa ya jinkirta.