✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba zai yiwu a mana abin da aka yi wa Barcelona ba- Marcelo

Dan wasan bayan Realmadrid da Brazil, Marcelo ya yi wa Barcelona shagube inda ya ce ba zai yiwu ba a samu kamar yadda aka yi…

Dan wasan bayan Realmadrid da Brazil, Marcelo ya yi wa Barcelona shagube inda ya ce ba zai yiwu ba a samu kamar yadda aka yi wa Barcelona inda suka doke Roma da ci hudu da daya a wasan farko, sannan Roma ta farke a wasa na biyu da ci 3 da nema wanda hakan ya sa suka kora Barcelona daga gasar.

Marcelo wanda shi ne ya zama kyaftin din Realmadrid a wasan a madadin Sergio Ramos, ya ce sun cancanci nasarar da suka samu, “mun yi duk abin day a kamata mu yi domin mu samu nasarar tsallakewa zuwa wasan kusa da karshe.

“Ba zai yiwu ba a mana yadda aka yi wa Barcelona saboda mu Realmadrid ne ba Barcelona ba,” inji shi.