Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) ta ce ba ta da shirin yin kowacce irin zanga-zanga a halin yanzu saboda karin kudin man fetur.
Sai dai kungiyar ta ce ta yi Allah-wadai da matakin da ta bayyana da “rashin imani da tausayi” da Gwamnatin Tarayya ta dauka ba tare da la’akari da wahalar da talakawa za su sha ba, amma dai yanzu ba za ta yi zanga-zanga ba.
Shugaban kungiyar na kasa, Kwamared Joe Ajaero, a cikin wata sanarwa da Kakakin kungiyar, Benson Upah, ya fitar, na mayar da martani ne kan wasu rahotanni da ake yadawa cewa kungiyar za ta tsunduma yajin aiki.
Aminiya ta rawaito cewa taron tattaunawar da aka yi tsakanin wakilan ’yan kwadagon da na Gwamnatin Tarayya a ranar Laraba ya tashi baran-baran.
Da yake karin haske kan matakin nasu na gaba, Kwamared Ajaero ya ce za su gudanar da taruka a ranar Juma’a domin tattauna batun karin kudin.
Ya ce, “An jawo hankalinmu kan wasu sakonni a kafafen sada cewa ’yan kwadago za su yi zanga-zanga [gobe] Juma’a saboda karin kudin mai.
“Duk da ba mu ji dadin abin da aka yi wa talakawan Najeriya ba, amma ba mu da shirin daukar wani mataki ranar Juma’a.
“Saboda haka muke kira ga jama’a da su yi watsi da irin wadannan labaran, ba daga wajenmu suka fito ba,” in ji shi.