✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugaba Tinubu ya yi ganawar farko da shugabannin tsaro

Sabon shugaban na ci gaba da ganawa da masu ruwa da tsaki don inganta gwamnatinsa.

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi ganawarsa ta farko da shugabannin tsaro da na leken asiri a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.

Babban Hafsan Tsaro, Janar Lucky Irabor ne ya jagoranci mahalarta taron da suka hada da Babban Hafsan Sojin Kasa, Laftanar-Janar Farouk Yahaya da Babban Hafsan Sojin Ruwa, Vice Admiral Awwal Gambo da Babban Hafsan Sojin Sama, Air Marshal Isiaka Amao dai kuma Sufeto-Janar na ’yan Sanda, Usman Alkali Baba.

Sauran su ne Darakta-Janar na Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS), Yusuf Bichi da Darakta-Janar na Hukumar Leken Asiri ta Kasa (NIA), Ahmed Rufa’i Abubakar.

A ranar Laraba ne shugaban ya gana da Shugaban Hukumar Yaki da Masu Yi Wa Tattalin Arzikin Kasa Zagon Kasa (EFCC), Abdulrasheed Bawa, a fadar shugaban kasa.