✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba za mu yi wa zabin ‘yan Najeriya katsa-landan ba a 2023 – INEC

INEC ta ce ba za ta yi wa 'yan Najeriya katsa-landan ba

Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya tabbatar da cewa, hukumar ba za ta yi wa iya kokarinta wajen ganin ba ta yi wa ‘yan Najeriya katsa-landan ba a zaben 2023 mai zuwa.

Yakubu ya bayyana haka ne yayin karbar tawagar da wakilin Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya kuma shugaban ofishinta mai kula da Yammacin Afirka da yankin Sahel (UNOWAS), Mahamat Saleh Annadif, ya jagoranta a hedkwatar hukumar da ke Abuja.

Da ya ke yaba wa UNOWAS kan gudummawar da ta ke ba wa hukumar zaben a manyan zabukan kasa, Yakubu ya tabbatar wa tawagar cewa za su ci gaba da kokari domin ganin an yi zaben 2023 lafiya ba tare da samun magudi ba.

Haka kuma ya ce a matsayin hukumar na wacce gudanar da sahihin zabe ya rataya a wuyanta, tana sane da muhimmancin da samar da dabarun zaman lafiyar Najeriya ke da shi ga sauran yankin Afirka ta Yamma ta fuskar gudanar da zaben.

Ya ce, “Na tuna yadda UNOWAS da gudunmawar da hukumar ta ba mu gabanin gudanar da babban zaben shekarar 2019″

“Duk lokacin da Najeriya ta gudanar da babban zabe, to tamkar zabukan gama-gari ne a fadin Afirka ta Yamma. Don haka, muna yabawa da gagarumin nauyi da aka dora wa hukumar.

“Kamar yadda kuka sani, kasashe 15 ne a yankin. Kuma domin nuna mahimmancin Nijeriya a tsarin dimokuradiyyar mu, ya zuwa wannan ranar muna da mutane miliyan 84 da suka yi rajistar zaben.

“Sai dai jimillar adadin wadanda suka yi rajista a sauran kasashe 14  ya kai miliyan 73, wanda hakan ke  nuna Najeriya ta haura  jimillar sauran kasashen yankin baki daya a yawan masu zaben,” inji Farfesa Yakubu.