Majalisar Dokokin Jihar Zamfara ta juya bayanta a kan umarnin Gwamnatin Tarayya na haramta tashi da saukar jirage da kuma hana ayyukan hako ma’adanai a Jihar.
A yayin zamanta na ranar Laraba, Majalisar ta ce ba za ta sabu ba game da matakin da Gwamnatin Tarayya ta dauka ta bakin Mai ba Shugaban Kasa Shawara kan Tsaro, Manjo-Janar Babagana Monguno.
- ’Yan bindiga sun yi garkuwa da mutum 50 a Zamfara
- Masu hakar ma’adinai sun nesanta kan su da ’yan bindiga
- Zamfara: Zan yi murabus idan za a samu zaman lafiya —Matawalle
Haka kuma, Gwamnatin Tarayya a wata sanarwar da Fadar Shugaban Kasa ta fitar ta ce kwararan dalilai sun nuna jiragen sama na yi wa ’yan bindgia dakon makamai.
Kakakin Shugaban Kasa, Garba Shehu ya bayyana wa Aminiya haka ne yayin bayani kan haramta shawagin jirage a Jihar Zamfara da Gawmanti Tarayya ta yi.
Sai dai ’yan Majalisar sun ce akwai rashin kyakkyawar fahimta da Mai Ba Shugaban Kasa Shawara kan harkokin tsaro ya yi wa kalubalen da jihar Zamfara ke fuskanta a halin yanzu.
Matakin hakan na zuwa ne yayin da Shugaban Majalisar Faruk Dosara ya gabatar da kudirin cewa hukumomin tsaro sun gaza musamman a bangaren amsa kiran neman agajin gaggawa.
Yayin ci gaba da tattaunawa a kan kudirin da Honarabul Dosara ya gabatar, mai magana da yawun Majalisar Mustapha Kaura, ya bayyana cewa akwai nakasu ta yadda ake tattara bayanan sirri da kuma raba su a tsakanin hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki.
Majalisar ta kuma bayar da shawarar cewa gwamnatin tarayya ba tare da wani jinkiri ba ta kafa wani kwamitin kwararru da za su gudanar da bincike gami da bitar tsare-tsaren tsaro na dukkan hukumomin tsaro a Jihar suka tanada.
Suna kuma kiran gwamnatin jihar da ta hanzarta kafa wani kwamitin na daban da zai gudanar da bincike domin gano masu lalata tsarin zaman lafiya da ke gudana a jihar ba tare da la’akari da bangarancinsu na siyasa ba.
Da yake babatu dangane da umarnin hana tashi da saukar jirage a Jihar, Honarabul Dosara ya ce wannan doka ba ta da wani tushe, inda ya ce satar dalibai ba daga jihar Zamfara aka fara ta ba.
Ya buga misali da cewa an yi garkuwa da dalibai a Chibok, Dapchi, Kankara da kuma Kagara, amma hakan bai sanya gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta yanke irin wannan hukuncin a jihohin da hakan ta kasance ba sai Jihar Zamfara kadai da aka sace dalibai a Jangebe.
Aminiya ta ruwaito cewa, Kungiyar Tuntuba ta Arewa (ACF), ta bukaci Shugaba Buhari ya fadada haramcin shawagin jirage a jihohin yankin da suke fama da matsalar tsaro.
Shugaban ACF, Cif Audu Ogbeh, ya ce akwai bukatar a haramta shawagin jirage a jihohin Borno, Neja, Taraba da Binuwai inda ake zargin jiragen sama na kai wa ’yan bindiga da mayakan Boko Haram makamai a cikin dazuka.