✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba za mu kara farashin kayayyaki ba a watan Azumi —BUA

Kamfanin ya ce daga yanzu zuwa bayan azumi ba zai kara farashin kayayyakinsa ba.

Shugaban Kamfanin BUA Alhaji Abdulsamad Isyaka Rabiu, ya yi alkawarin cewar ba zai kara farashin kayayyakin kamfanin ba a lokacin watan azumi.

Shugaban kamfanin na shiyyar Arewa, Alhaji Muhammadu Adakawa ne ya bayyana haka ga manema labarai a Kano.

Ya bayyana cewar shugaban kamfanin ya bai wa abokan hulda umarnin kada su kara farashin kayayyaki tun daga yanzu zuwa bayan watan azumi da ke karatowa.

Alhaji Adakawa, ya yi bayanin cewae a baya-bayan nan an samu wasu da suka yi karin N1,500 kan kilo 50 na sukari, amma ya bai wa abokan hulda tabbacin cewar kamfanin ba zai yi karin farashin kayayyakinsa ba.

“A wannan shekara hukumar gudanarwar kamfanonin BUA sun duba muhimmancin yadda abubuwa suke, inda ta roki abokan hulda da ita a kan kada su yi karin farashi musamman na sukari.

“Don haka aka umarce ni na sanar da al’umma cewar daga yanzu har zuwa bayan watan azumi ba za a yi karin farashi a kan kayayyakin kamfanin BUA ba,” in ji shi.