✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ba za mu daina amfani da tsoffin kudi ba —El-Rufai ga Buhari

El-Rufai ya ce tsawaita wa’adin amfani da N200 da Buhari ya yi ba tare da ya hada da N500 da N1000 ba, rashin biyayya ne…

Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ce za a ci gaba da amfani da tsoffin takardun Naira a jiharsa sabanin umarnin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

A ranar Alhamis, ta cikin jawabin kai-tsaye da ya yi wa ’yan Najeriya, Buhari ya ce tsoffin takardun N500 da N1000 sun daina aiki a fadin kasar; Tare da cewa, duk masu ragowar tsoffin kudin su kai wa Babban Bankin Najeriya (CBN).

Sai dai kuma, a jwabin da ya yi wa ’yan jiharsa daga baya a ranar, El-Rufai ya ce jiharsa za ta ci gaba da amfani da tsofiin kudi zuwa lokacin da Kotun Kolin za ta yanke hukunci kan shari’ar da ke gabanta.

A cewar El-Rufai, “Domin kore shakku, za a ci gaba da amfani da tsoffin takardun Naira a Jihar Kaduna zuwa lokacin da Kotun Koli Najerya za ta yanke hukunci.

“Don haka ina kira ga al’ummar Jihar Kaduna da su ci gaba da amfani da tsoffin kudi ba tare da wani tsoro ba.

“Jihar Kaduna da hukumomi za su rufe duk inda aka ki karbar tsoffin kudin a kuma hukunta su,” in ji shi.

Ya kara da cewa, tsawaita wa’adin amfani da N200 da Buhari ya yi ba tare da ya hada da N500 da N1000 ba, rashin biyayya ne ga Kotun Koli.

Ya ce, Gwamnatin Tarayya ta gabatar wa gwamnatocin jihohi tayin tsawaita N200 ne kwana uku kafin jawabin Buhari na ranar Alhamis.

“Kuma an ce musu tsawaita wa’adin ya takaita ne a kan N200 kawai saboda an riga da an lalata tsofin takardun N1,000 da N500 da suka koma bankuna.

“Ba mu yarda da tayin ba, kuma mun bayyana hujjoji kan tsoffin kudin na nan ba a lalata su ba,” in ji shi.

%d bloggers like this: