Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa gwamnatin tarayya za biya mafi karancin albashin da ba zai gagare ta ba.
A jawabinsa Shugaban kasar a lokacin bikin Ranar Dimokuradiyya ya sanar da Majalisar Dokoki ta kasa cewa nan ba da jimawa ba zai aike mata takardar dokar sabon mafi karancin albashi na kasa.
Daga bisani ya ta yi wani jawabin a daren Larabar a dakin taro na gidan gwamnati dake Abuja, a lokacin liyafar bukin bukin cika shekaru 25 na ranar dimokuradiyya.
Da yake magana kan batun mafi karancin albashi ga shugabannin majalisar dokokin kasar, wanda shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya wakilta, shugaba Tinubu ya ce gwamnati za ta yi abin da ya kamata, amma abin da za ta iya za ta biya.
- Ma’aikatan Najeriya miliyan 71 ba za su samu karin albashi ba
- An kama shi da kokon kawunan mutane takwas
“Shugaban Majalisar Dattawa, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, za ku sami sanarwa kan mafi karancin albashi. Za mu yi abin da Najeriya za ta iya, abin da za mu iya, ba abin da ake so ba, za mu yi daidai ruwa daidai kurji,” in ji Shugaban.
Rusunawa na yi ba faduwa ba
Game da maganganun da ke yadawa a soshiyar midiya geme da faduwar da ya yi a mota a wurin bukin Ranar Dimokuradiyya, shugaban kasar ya ce, “dobale”, ya yi, wato rusunawa da harshen Yarbanci.
A cewarsa, a matsayinsa na Bayarbe, dobale ya yi a Dandalin Eagle Squere, kuma dimokuradiyya ta cancandi a rusuna mata.
“Ranar 12 ga watan Yuni tana wakiltar zuciya da ruhin gwagwarmayarmu ta dimokuradiyya a kasar nan.
“Da sanyin safiyar yau, na samu tuntube wanda ya karade shafukan sada zumunta.
“Sun rude, sun kasa gane shin rawar buga ce ko rawar babbar riga, amma ranar bikin dimokradiyya ce, ni kuma na ya ‘dobale’ domin Dimokradiyya.
“Ni Bayarbe ne, a al’adance na yi dobale na. Ranar Dimokuradiyya rana ce da ta cancanci faduwa,” in ji shi.