✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba za mu bar matanmu su fita tsirara don tabarbarewar tsaro ba – Sheikh Bala Lau

A kwanakin baya ne aka fara samun kai hare-haren bam da ake zargin ‘yan mata sanye da hijabi na yi musamman a Jihar Kano, lamarin…

A kwanakin baya ne aka fara samun kai hare-haren bam da ake zargin ‘yan mata sanye da hijabi na yi musamman a Jihar Kano, lamarin da ya jawo wasu ke kokarin daina sanya hijabi wasu kuma na kiran a hana sanya hijabin. A tattaunawarsa da Aminiya Shugaban kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’a Wa Ikamatis Sunnah ta kasa Sheikh Abdullahi Bala Laub ya ce tabrbarewar tsaro ba za ta sa Musulmi su bar matansu su rika fita tsirara ba. Kuma ya ce komawa ga Allah ce kawai za ta fitar da kasar nan daga mugun halin da take ciki:

Aminiya: Matsalolin tsaro na kawo barazana ga mata masu sanya hijabi, har wasu na kiran gwamnati ta dauki mataki, yaya kake ganin wannan al’amari?
Sheikh Bala Lau: Babu shakka halin da muka samu kanmu na tabarbarewar tsaro a kasar nan, yana bukatar komawa ga Wanda mallakar tsaro da zaman lafiya Yake wurinSa  Shi ne Allah. Ya kamata tunaninmu ya canja kowa ya koma ga Allah. Kan wannan matsala gwamnati ta ware makudan kudi, bangaren tsaro shi ke da kaso mafi tsoka a kasafi, amma har yau abin bai tsaya ba kullun karuwa yake, abin bai tsaya ba ya neman mamaye Arewa  maso Gabas. Abin ya shafi kowa kada ya tsaya kawai ga hukuma, ya kamata kowa ya shigo ciki ta yaya za a shigo ciki, akwai abin da ya kamata shi ne, Allah Yake mallakar komai da kowa, Ya kamata mu koma zuwa gare Shi, mu kaskantar da kai mu tuba, mu roke Shi mun yi laifi, daga shugabanninmu da talakawa da malamai da attajirai, kowa na da abin da ya yi kuma kowa na da gudunmawar da zai iya badawa don tabbbatar da zaman lafiya. Bayan nan mu dage da addu’o’i, idan ana addu’a babu abin da ba za a iya samun saukinsa ba, duk abin da Allah Ya kawo komai tsananinsa Yana iya saukake shi.
Na biyu kuma kan abin da ya shafi  hijabi , idan jami’an tsaro suka ce za su dauki mataki kan hijabi, to Wanda Ya ce a sanya hijabin nan Shi ne ya ce a yi Sallah sau biyar a rana,Wanda Ya ce mata su sanya hijabin nan, Shi ne Ya ce a yi azumin Ramadan,Wanda Ya ce a sanya hijabin nan, Shi ne Ya ce a yi aikin Hajji. Musulunci addini ne wanda ya shiga ko’ina, don haka a gano wanda ya yi  laifi, amma kada a fito a yaki wani abu da Allah Ya ce a yi ko Manzon Allah (SAW) ya ce a yi, a ce za a hana. Akwai kasar da ta yaki hijabi amma ba ta zauna lafiya ba, saboda haka ina sanar da hukumomi cewa duk wanda ya ce zai hana sanya hijabi kamar ya hana mu yin Sallah ne, saboda haka ba zai zauna lafiya ba. Mu masu roka wa kasarmu zaman lafiya ne, sai dai duk abin da Allah Ya dora mana, to dole mu bi shi. Akwai alamomi na addini da ake amfani da su da yawa don a cutar da Musulmi, misali kowa ya karanta a jaridu cewa an kama mutane ba daya ba, ba biyu ba  da alamomi na addini za su kai hari a wuraren ibadar Kiristoci, an samu wani da rawani an samu wasu ta hijabi da dai wasu alamomi, amma ba Musulmi ba ne, me ake so a yi? Ana so ne a bata wa Musulmi da Musulunci suna, Musulunci bai yi umarni da irin wannan ba. Don haka ina kira ga shugabanni su gane irin wannan, kada a  tsokani Allah, duk abin da Ya dora mana, a bari mu yi, tunda akwai hanyoyi da suke da su na dabarun gano masu laifi, su yi kokari bin su don gano masu  laifin, kada a taba hijabi  kada a ce  za a hana sanya hijabi. Ke nan ana nufin matanmu su fito tsirara, mu bar ’ya’yanmu su fito tsirara don akwai tabarbarewar tsaro, lallai wannan ba zai yiwu ba. Kuma kamar yadda ake kai hari da hijabi da rawani da sauransu, ya kamata hukumomi su san cewa ana kai hari da yunifom din ’yan sanda da na soja, to ke nan za a hana ’yan sanda da soja sanya rigunansu. An sha ganin motoci da alamu na sojoji ana kai hari da su, saboda haka hukumomi suna da gagarumin kalubale a gabansu, kada su zauna da dabararsu da wayonsu su koma ga Allah. Malaman addini da masu wa’azi duk jama’a a koma ga Allah, don ya ce “Fal ya’abudu rabba hazal bait. Allazi adda’amahum minju’in wa amanahum min haufin.” Mutanen Makka sun zauna cikin tsoro da firgici, sai Allah Ya ce maganin matsalar shi ne su bauta wa Ubangijin Ka’aba, ku kadaita Shi, da suka kama bautarSa sai suka samu zaman lafiya da walwala Ya kore musu yunwa, har abada arzikin da Allah Ya ba ta  da zaman lafiya, duk  duniya babu inda ya kai Makka zaman lafiya. Kwanan nan na ji sun dauki Dala miliyan 100, Majalisar dinkin Duniya don samar da zaman lafiya, kafin nan sun taba ba da Dala miliyan 500 don tallafa wa zaman lafiya, ya kamata mutane su gane cewa idan ka bi Allah sai Allah Ya ba ka zaman lafiya.
Aminiya: Ko kun taba ganawa da shugabannin kun ba su shawara kan abubuwan da suke neman tasowa?
Sheikh Bala Lau: Matsayinmu na  masu karantarwa muna da hanyoyi da yawa da muke amfani da su don wa’azartarwa, duk inda muka yi wa’azi muna isar da wadannan sakonni, wurin hudubobinmu a masallatan Juma’a muna isar da sakonnin, gwamnati tana da jami’anta har cikin ’yan jarida, wadanda duk abin da muka yi za su je su kai musu, babu inda za mu yi taro mu kai 100n a ce gwamnati ba ta san abin da muka yi ba. Har cikin ’yan agaji an sanya mana masu kai rahotanni, gwamnati ta san abin da muke yi don ba mu yin a boye, sannan muna da hanyoyi  kamar na wasiku da wadanda muke da kyakkyawar alaka da su, muna samun lokaci mu zauna mu ce ga shawarwarinmu su dauka , sai dai daukar mataki kuma ya rage nasu.
Aminiya: Abin da ke damun jama’a shi ne an kashe Sheikh Ja’afar an nada kwamiti an kashe Sheikh Albani an nada Kwamiti ga shi an kai wa Sheikh dahiru Bauchi hari an kashe wasu, an kai wa Buhari hari, ga shi kwanan nan an kashe ’ya’yan Sheikh Ibrahim Zakzaky, shi ma an ce an kafa kwamiti, ba ku tunanin wata rana mabiyanku su botsare su dauki doka a hannunsu?
Sheikh Bala Lau: Wannan gwamnati ne ya kamata ta dauki mataki ba ma na irin wannan da aka ambata  ba, kusan abin da Najeriya ta gada ke nan a ta da hankali a kafa kwamitoci a yi bincike kuma ba a yin komai . Wannan ba ya kawo wa kasa zaman lafiya, idan kullum za a kama mai laifi ba za a hukunta shi ba, kamar ana ba masu aikata laifin lasisi ne su je su yi laifi. Saboda haka muna kira ga gwamnati ta mai da hankali kan wannan. Duk masu hankali suna bibiyar abubuwa, babu abin da ya fi hadari kamar taba malaman addini, idan ana dauki daidai yau a kashe wannan gobe a kashe wancan, to lallai ana kara jefa kasa cikin tabarbarewar tsaro, ana iya kaiwa masu addini ba za su iya hakuri su jure ba, duk lokacin da aka taba musu malami.
Kamar yadda ka ambata an kashe Sheikh Ja’afar an kashe Sheikh Albani, an kai wa Sheikh dahiru Bauchi da Janar Buhari hari, kuma kwanan nan an kashe ’ya’yan Sheikh Ibrahim Zakzaky da sauransu, wannan ba alheri ba ne, ya wajaba gwamnati ta sanya ido a kan wannan, duk inda ake taro na addini ya kamata a sanya ido a sanya tsaro, domin a samu cikakken zaman lafiya. Kuma lura da halin da ake ciki malamai suna da gagarumar gudunmawar da suke ba da badawa, wurin tabbatar da zaman lafiya. Sau da yawa  wasu suna daukar malamai abokan gaba, musamman idan za su fito su yi wa’azi a kan abubuwan da suke yi marasa kyau, sai su dauke su abokan gaba.  Idan ana kai hare-hare a kansu ba zai taimaka wajen zaman lafiya ba, idan ka kau da wannan ko ka tsare wancan ba zai taimaka ba wajen kawo zaman lafiya ba. Allah zai sake fito da wasu da suka fi wadancan, zaman lafiyarka ka ci gaba da karbar wa’azi, ka gyaru, idan ka gyaru, ka zama na kwarai sai Allah Ya sanya wa shugabancinka albarka. Ina kira ga wadanda Allah Ya shugabantar a kan jama’a su san nauyin da ke kansu. Shugabnci yana tare da nadama da abubuwa da dama, idan ka samu dama ba ka yi amfani da ita ba, lokacin da ta wuce za ka yi da-na-sani. Idan ka yi barna Allah ba zai bar ka ka zauna lafiya ba. Lokacin da ka samu dama ka kulla alaka mai kyau da Allah, ka yi kokari ka tallafa kuma ka taimaka wa jama’a.
Allah Yana jarraba mu da fitintinu iri-iri a kasar nan da suke faruwa sakamakon abin da muke aikatawa, idan mun tuba sai Allah Ya ba mu zaman lafiya. yanzu ga masifar cutar Ebola da ta shigo cuta ce da ba a gano maganinta ba, kuma ana kokarin a hana mutane gaisawa da juna musabaha. Idan ka gaisa da dan uwanka wai za ka dauka ga shi Musulunci ya yi umarnin a rika musabaha, don haka ya kamata mu fahimci cewa zaman lafiyarmu da Allah ita ce mu koma ga Allah. Ana maganar Boko Haram duk da irin dubban rayukan da ake rasawa an koma kan Ebola, gwamnati za ta dauki kudi ta kashe don kawar da Ebola, idan muna da hankali mu komaw ga Allah don Shi ne maganin duk wata matsala.
Aminiya: A matsayinku na malamai ko kun taba haduwa kuka yi shawarar fito da wata jam’iyya ta Musulunci da za a ce al’ummar Musulmi za su ba da goyon baya gare ta?
Sheikh Bala Lau: Lallai ba mu da wannan shiri na fito da wata jam’iyya ta Musulmi, Najeriya Allah Ya ajiye ta akwai Musulmi da wadanda ba Musulmi ba, saboda haka duk jam’iyyun da muke da su akwai Musulmi akwai wadanda ba Musulmi ba. Abin da muke yi shi ne ina mutumin kirki yake, in da mutumin kirki yake shi ne a yi kokari a zabe shi domin ya fidda al’umma daga cikin halin da take ciki na wahala. Na tabbata da Musulmi da Kirista ba sa jin dadin abin da ke faruwa a yanzu na kashe-kashe na zub da jinin al’umma, babu addinin da ya yarda da wannan. Kuma Allah Ya ajiye mu tare, dole mu yi hakurin zama tare, don haka kada a rude mu a shigar mana da wasu abubuwan son zuciya ko na son duniya. Mu zabo mutanen kirki, har Allah Ya taimake mu da jagorori na kirki a samu canji mai ma’ana a kowane mataki.
Aminiya: Yaya za ka bayyana yadda kake ji game da shugabancin wannan kungiya ta Izala?
Sheikh Bala Lau: Kan batun shugabanci zuwa yanzu ina cike da farin ciki da Allah Ya kawo ni wannan matsayi ba dabarana ba ba wayona ba. Babban abin jin dadina shi ne samun hadin kan abokan aikina, don ba zan iya aikin ni kadai ba, dukan malaman da muke tare da su muna samuin cikkakken hadin kai, ina za mu dauki wannan kungiya mu kai ta mataki na gaba, ba ni nakey i ba, tare muke haduwa mu yi. Yaya  alakar wannan kungiya da sauran kungiyoyi a Najeriya, muna kokarin mu ga an samu cikkakken hadin kai, ba ma da sauran kungiyoyi ba, har da alakar wannan kungiya da sauran kungiyoyin addini na duniya. Muna kokarin mu kai ga yadda wannan kungiya za ta tsaya ta dogara da kanta bayan dogaronta ga Allah. Shi ne abin da muke fuskanta ya zama ba mu barace-barace, duk in da aka gan mu a gan mu da mutunci da daraja. Sai yadda za mu tallafa wa masu raunin da ke cikinmu, ba tare da da’awarmu ta canja daga yadda aka santa ba, mu fito da salo na da’awa saboda Bahaushe ya ce da’awa sai da dawa idan babu dawa za a shiga dawa daga nan sai a fara adawa kuma babu dawowa.