Kwamitin Kar-ta-Kwana da Shugaban Kasa ya kafa kan yaki da cutar COVID-19 ya gargadi mara sa takunkumi cewa ba za a bar su su kada kuri’a a zaben gwamnan jihar Ondo na ranar Asabar ba.
Babban jami’in kwamitin, Dakta Sani Aliyu shine ya bayyana hakan ranar Alhamis a Abuja yayin jawabin da kwamitin ya saba gudanarwa.
- Zaben Ondo: INEC ta raba muhimman kaya
- Zaben Edo da Ondo: Birtaniya za ta sa wa masu rikici takunkumi
Ya gargadi dukkan masu zabe, ‘yan takara da jami’an Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) kan su kiyaye dokokin da hukumomin lafiya suka gindaya a rumfunan zabe.
Sai dai ya yi kira ga jam’iyyu 17 da za su shiga zaben da su bayar da hadin kai wajen tabbatar da nasarar shiye-shiryen da aka yi a zaben.
Ya ce ba zai yuwu kasar ta yi kantafi da nasarar da ta samu a yaki da cutar yayin zaben jihar ba.
Dakta Sani ya ce za su tabbatar an samar da kayan kariya ga dukkan jami’an zabe yayin da za a yi wa dukkan kayan aikin zaben feshin kashe kwayoyin cututtuka.
Ya ce, “Dangane da zaben Ondo na ranar Asabar kuwa, muna sa ran akalla masu kada kuri’a miliyan daya da rabi ne za su yi zabe a mazabu 3,000 dake fadin jihar.
“Hakika wannan babban aiki ne mai cike da hadarurruka. Saboda haka, domin mu tabbatar mun ba masu kada kuri’a, masu aikin zabe, da ma ‘yan takara kariya, dole mu tabbatar cewa an bi matakan da aka tanada yayin zaben.
“Takamaimai, dole ne kowa ya yi amfani da takunkumin rufe fuska domin ba za a bar mara sa shi su yi zabe ba, kuma a bayar da tazara yayin tsayawa a layin zabe.
“Za a samar da sinadaran tsaftace hannuwa, kuma za a yi layi har hawa biyu; na ciki da na waje.
“Za a rika shigar da masu zabe zuwa layin ciki daga layin waje daga lokaci zuwa lokaci domin gujewa cinkoso, kuma za mu rika yin feshi a kayan zaben a kai a kai, tare da samar da na’urar gwajin zafin jiki a kowacce rumfar zabe,” inji Dakta Sani.
Babban jami’in ya kuma ja hankalin dukkan masu ruwa da tsaki kan harkan zaben cewa babban burin gwamnati shine kiyaye rayuwa da lafiyar al’umma, yana mai kiransu kan su ba da goyon baya domin ganin komai ya tafi kamar yadda aka tsara.