✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba Shugaban kasa ya gina Masallacin Sheikh dahiru Bauchi ba – Sayyadi Ibrahim

Shugaban Gidauniyar Sheikh dahiru Usman Bauchi Sayyadi Ibrahim Sheikh dahiru Bauchi ya musanta jita-jitar da wasu jama’a ke yadawa cewa Shugaban kasa Goodluck Jonathan ne…

Sheikh Dahiru Usman BauchiShugaban Gidauniyar Sheikh dahiru Usman Bauchi Sayyadi Ibrahim Sheikh dahiru Bauchi ya musanta jita-jitar da wasu jama’a ke yadawa cewa Shugaban kasa Goodluck Jonathan ne ya sake ginin masallacin Sheikh dahiru Usman Bauchi da ke Tudun Wada Kaduna.
Sayyadi Ibrahim dahiru Bauchi ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kaduna inda ya ce wani bawan Allah da ba ya son a ambaci sunansa ne ya gina masallacin, ba Shugaba Jonathan ba. “Wani bawan Allah kuma Minista ne ya dauki nauyin yin aikin fisabilillahi, kuma ya bukaci a sakaya sunansa,” inji shugaban.
Ya ce a yayin da ake neman taimakon sake ginin masallacin ne ministan ya samu labari, kuma ya yi alkawarin gina shi a cikin wata hudu zuwa biyar, ganin cewa watan Azumi ya karato, ana so a yi tafsirin bana a ciki, kuma Allah Ya ba shi ikon gamawa cikin wannan lokaci.
Sayyadi Ibrahim, ya ce wannan bawan Allah da ya gudanar da aikin masallacin, ya taba gina wani masallacin da Shaihin ke amfani da shi a garin Bauchi, kafin ya zo ya gina wannan masallacin da ke Kaduna. “Duk da yake shi wannan bawan Allah minista ne, ya taba zama daya daga cikin daliban Shaihi din a baya, kuma ya gudanar da aikin ne fisabilillahi kuma don Allah da neman lada, kuma yanzu haka ba mai zuwa wajen Shaihin ba ne a kai-a kai, amma sai dai suna yin waya da junansu.”
Har ila yau, a cewar Sayyadi Ibrahim, aikin ginin masallacin Shaihin da ke hade da makaranta a Unguwar Bakin Ruwa a kan babbar hanyar zagaye ta garin Kaduna, wani dan kasuwa abokinsu ne da ke Kaduna  ke ginawa shi kadai, kuma shi ma ya bukaci a sakaya sunansa, domin yana yin aikin ne don neman lada a wurin Allah.
Ya ce a yanzu da ake gudanar da azumin watan Ramadan akwai bukatar Musulmi su yawaita yin salatin Annabi da istigifari a kullum. “Ko sau dubu bayan kowace Sallah ta farilla ko akalla istigifari dubu biyar duk yini ko dare musamman a cikin lokacin azumi, don mu ga kowane irin alheri ne zai shigo mana kasa, saboda istigifari na yaye bala’i,” inji shi.
Sayyadi Ibrahin dahiru Bauchi, ya gode wa al’ummar Musulmin da suka halarci taron bude masallacin, musamman Sarkin Musulmi da Gwamnan Jihar Kaduna da Shehun Borno da Sarkin Birnin Gwari da sauran al’ummar Musulmi.
A ranar Juma’ar da ta gabata ce aka bude masallacin, kuma a wannan rana ce Sheikh dahiru Usman Bauchi ya fara gudanar da tafsirin azumin bana.