✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba ni na kashe zomon ba: Sharhin littafin dakika Talatin (2)

Sunan littafi:          Dakika TalatinMarubuci:          Ado Ahmad Gidan DabinoShekarar Wallafa:          2015Kamfanin Wallafa:          Gidan Dabino Publishers, KanoFarashi:               Ba a fada ba…

Sunan littafi:          Dakika Talatin
Marubuci:          Ado Ahmad Gidan Dabino
Shekarar Wallafa:          2015
Kamfanin Wallafa:          Gidan Dabino Publishers, Kano
Farashi:               Ba a fada ba

Wannan takaddama ta sa Aminu bai fita daga zargin da ake yi masa ba, domin ta kai har danginsa ma ba sa musun cewa shi ne ya yi wa Zannira ciki. Dangantaka tsakaninsa da budurwarsa Amina wadda zai aura kuma babbar aminiyar Zannira ta fara yin tsami, sakamakon zuga ta da Samira tsohuwar budurwar Yassar ta rika yi.
Ganin ana neman sheganta wa Zannira cikin da take dauke da shi, ya sa ta shigar da kara gaban alkali don yi wa tufkar hanci tun ba ta haife ba. Da alkali ya nemi jin ta bakinta kan inkarin da masu hakkin cikin suka yi sai ta ce: “Abin da zan ce, Allah Ya ba ka nasara shi ne, ai ni ce shaida, tun da ni abin ya faru gare ni ba wata ba. Kuma ai ba abu ne da ake yi a bainar jama’a ba, balle a ce sai kowa ya ji ya gani, abu ne na sirri, sai kuma daga baya ne yake bayyana har jama’a su gan shi, ga shi kuma ya bayyana lokacin da jama’a za su gan shi.
“Kuma wannan abu ya faru ne ranar da aka daura mana aure a gidansu, a dakinsa kuma wasu daga cikin abokansa sun ga lokacin da muka zo ni da kawata Amina, sannan ita ma Amina shaida ce.” (Shafi na 93).
Bayan kotu ta saurari shaidu, wadanda suka hada har da kawarta Amina da suka ziyarci Yassar tare, Inna Mai Koko ta kekasa kasa kan cewa duk hadin baki ne don a nasabta su da shege, har sai da aka gayyato likita kotun, ya yi cikakken bayani filla-filla kan yadda ciki kan samu, da ma yadda yakan rayu har a kai ga haihuwarsa. Nan take jikin kowa ya yi sanyi a kotun, har da Inna Mai Koko. Daga karshe alkali ya fitar da hukunci da cewa: “Inna Mai Koko, wannan yarinya za ku ci gaba da kula da ita, kuma idan ta haihu ma za ku yi duk abin da ake yi wa kowace mai jego, sannan kuma abin da za ta haifa yana da gadon marigayi Yassar, ita ma Zannira tana da tumunin takaba, tun da ya rasu ya bar ta da aurensa a kanta. Kuma daga ranar da ta haihu ta gama takabarta, tana iya yin aure in ta sami miji.” (Shafi na 103).
Bayan Zannira ta haihu har ta ya da wanka, kungiyarta ta horar da nakasassu sana’o’i ta samu bunkasa sosai, al’amarin da har ya kai ga ta samu karramawa daga gwamnati, a wani babban taron kungiyar da aka yi wanda har Kwamishinar al’amuran mata ta halarta da kanta. A cikin jawabinta ne ma take cewa: “Babban abin farin ciki ne a ce yau a jiharmu an sami mace wadda take gurguwa ce, amma tana koyar da mutane sana’o’i da kuma dogaro da kai. Wannan ya dada tabbatar mana da sunan kungiyar tasu, ‘Babu Nakasasshe Sai Kasasshe.’ Muna fata a sami irin Zannira da yawa a cikin jihar nan tamu, babu shakka za a ga abubuwan al’ajabi nan da ’yan shekaru.
“Babu shakka muna alfahari da ke Zannira a wannan jiha tamu. Saboda haka ne gwamnatin jiha ta ce a ba ki tallafin kudi Naira Miliyan goma don ki dada fadada wannan aiki naki na kungiya.” (Shafi na 107-108).
Salo: Marubucin wannan wasan kwaikwayo ya yi amfani da mikakken salo kuma mai armashi wajen isar da sakonsa, tun daga yadda ya kulla zaren labarin har zuwa kalmomin da ya zabo ya yi amfani da su; al’amarin da ya sanya labarin kasancewa mai dadin bibiya yayin karantawa, amma fa ga Bahaushe ko wanda ya nakalci harshen Hausa sosai. Domin duk da saukakan kalmomin da mawallafin ya yi amfani da su, ya zarge su da dimbin karin magana da ya sassarkafa cikin zantukan ’yan wasan, har mai wannan nazari ke ganin in ban da littafin Tabarmar Kunya na Dauda Kano da dangogo, ba a yi wani littafin wasan kwaikwayo da aka sarrafa karin magana cikinsa sosai kamar wannan littafi ba. Akwai jimlar mabambantan karin maganganu har guda 51 da marubucin ya yi amfani da su cikin littafin, ban da wadanda aka maimaita. Don haka muna iya cewa wannan littafi wata karamar taska ne na karin maganar Hausa.
Babu aron bakin kalmomi sosai cikin littafin. Hasali ma, a wurare biyu kacal za mu iya cewa ya yi amfani da kalmomin Ingilishi: “So what in ta mutu?” (Shafi na 22). “Ok, ya yi kyau.” (Shafi na 66).
A ganin mai wannan nazari, za a iya sanya kalmomin Hausa a guraben ba tare da dandanon zancen ya salamce ba.
Salon rayuwar da aka nuna cikin littafin irin na Hausawan yau ne, amma wadanda ba su yi watsi da kyawawan al’adun Hausawa ba. Wannan a fili yake in muka yi la’akari da yadda umurnin iyaye da biyayya gare su ya taka rawa sosai wajen zartar da duk al’amuran da suka gudana cikin wasan, tun daga neman aure har zuwa gaban alkali yayin shari’a. Dubi yadda Inna Mai Koko ta zamo ita ce uwa da makarbiya wajen kare dangin Yassar da suke zargin za a shigar musu da shege cikin zuri’arsu: “Ina rokon kotu ta hana wannan yarinya alakanta danmu da cikinta don ba namu ne ba kuma hankali ba zai yarda da wannan bayani nata ba, don ya saba wa hankali da tunani nesa ba kusa ba. Kuma ba mu da shaidar hakan ta faru a tsakaninsu. (Shafi na 93).
Dubi kuma yadda Zannira ta shirya gudanar shagalin bikinta: “Sannan mu yi ’yan kide-kide namu na mata, zan yi wani irin kunshi da na ga kawata ta yi ranar aurenta, da kitso. (Shafi na 25-26).
Duk da wannan, marubucin ya nuna wasu bakin al’adu da ba na Hausawa ba ne, wadanda a ganin mai wannan nazari rashin ambatar su ba zai rage komai daga armashin labarin ba. Kamar zuwa hutun watan zuma irin na Masihawa (Honey Moon – shafi na 26), da al’adar cewa “Lady First” (shafi na 25).
Tauraro: Tauraruwar wannan wasan kwaikwayo ita ce Zannira, domin da magana kanta aka fara wasan. Ita ce ta fuskanci duk wata gwagwarmaya da kalubale da suka faru a cikin wasan, tun daga farko har zuwa karshensa, inda ya kare da samun nasararta a kotu, tare da cin ma burinta na ganin kungiyar da ta kafa don horar da nakasassu da sauran mabukata hanyoyin dogaro da kai da barin mummunar dabi’ar kaskanci ta dogaro da samun wasu ya tabbata.
Halayen wasu ’yan wasa, kamar yadda aka nuna a cikin wasan:
Yassar: Tauraron wasan mai gajeren kwana. Matashin saurayi dan boko, amma wanda dabi’un boko ba su juyar da tunani da dabi’unsa ba. Mai kishin zuci, marar kyamar mutane, mai tsayawa kyam kan abin da ya yi imani da shi, mai biyayya ga magabatansa.
Aminu: Babban abokin Yassar. Nagartaccen saurayi, mai ikhlasi da rikon amana, mai tausayi, mai tawakkali. Yana da ’yar gafala kadan.
Amina: Babbar kawar Zannira. Amintacciya, mai hakuri, tana da saurin daukar zuga, amma tana da yafiya ga wanda ya saba mata.
Samira: Budurwar Yassar ta biyu, mai tsiwa da matsanancin kishi. Mai kokarin ganin ta cin ma burinta ta kowace hanya.
Inna Mai Koko: Kakar Yassar, mai tsattsauran ra’ayi da kishin dangi. Mai fadi a ji cikin iyali. Gwanar iya sarrafa zance da kokarin toshe duk wata kofa da za ta ba abokin karawarta nasara. Mai yarda da kaddara yayin da hujjojinta suka kare.
Ka Fi Rediyo: Sankira (maroki a wajen taruka). Gwanin iya barkwanci da zuga mutane don samun abin hannunsu. Dubi inda yake cewa: “Jama’a taro fa ya yi taro, daga jihohi daban-daban an zo daurin auren Yassar da Zannira mutanen kirki. Allah Ya sa ku ma masu halartar taron ku zama mutanen kirki ku ba ni rabona, kada taro ya tashi ku tashi da ni. E mana. In ba ku ba ni ba ai kun tashi da ni, ba ni ga tsuntsu ba ni ga tarko!” (Shafi na 35).