✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ba ni da aniyar tsayawa takarar Shugaban Kasa a 2023 – Buratai

Buratai ya ce bai taba nuna sha’awar tsayawa takarar ba, ballantana ma ya sa a lika fastocinsa.

Tsohon Babban Hafsan Sojojin Kasa na Najeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai (mai ritaya), ya nesanta kansa da wasu fastocinsa da suka fara yawo, wadanda ke alamta cewa zai tsaya takarar Shugaban Kasa a 2023.

Buratai, wanda kuma shi ne Jakadan Najeriya a Jamhuriyar Benin ya ce bai taba nuna sha’awar tsayawa takarar ba, ko ya tattauna da wani, ballantana ma ya ba da umarnin lika fastocin nasa.

Ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da tsohon Kakakin Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya, Birgediya Janar Sani Usman Kuka-Sheka (mai ritaya), ya fitar ranar Lahadi, inda ya yi kira da jama’a da su yi watsi da su.

Sanarwar ta ce, “Wannan kururuwar Iblis ce da wasu suke yada wa saboda wasu dalilan da su kadai suka sani.

“Mai girma Buratai na jaddada goyon bayansa ga ci gaba da hidimta wa kasa, a matsayinsa na Jakadan Najeriya a Jamhuriyar Benin yanzu haka.

“Yana nan tare da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari kuma yana godiya da damar da ya ba shi ta hidimta wa kasa,” inji sanarwar.