✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba ni da alaka da kowace jam’iyyar siyasa —Onochie

Ban kasance mamba ga kowace jam’iyyar siyasa ba a fadin kasar nan.

Hadima ta musamman ga Shugaba Muhammadu Buhari kan harkokin dandalan sada zumunta, Lauretta Onochie, ta yi watsi da zargin alakanta ta da jam’iyyar APC da ake yi.

Onochie, ta musanta ikirarin da ke cewa ita mamba ce ta jam’iyyar yayin da a ranar Alhamis take amsa tambayoyi a gaban kwamitin hukumar zabe na Majalisar Dattawa.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ’yan majalisar ke tantance Onochie a matsayin daya daga cikin Kwamishinonin Hukumar Zabe (INEC) da za ta wakilci Jihar Delta.

Bangarori da dama ciki har da jam’iyyar adawa ta PDP, sun zargi Onochie da cewa tana da katin shaidar zama ’yar jam’iyyar APC mai mulki a kasar, lamarin da suke kiran nada ta Kwamishina a Hukumar INEC ya ci karo da doka.

Sa dai Onochie ta musanta zargi, inda ta ce ba ta da alaka da kowace jam’iyyar siyasa a kasar.

A cewarta, “A tsawon shekaru dama, na fahimci muhimmanci gudanar da aiki bisa la’akari da tsari da kuma kiyaye duk wani tanadi na doka.

“Kuma a tsawon shekarun na yi hakan ne ba tare da nuna wata wariya ko banbanci ba ballanta kuma riko da wata akida ta siyasa.

“Tun daga shekarar 2019 har kawo yanzu, ba ni da wata alaka da kowace jam’iyyar siyasa ciki har da kungiyoyi masu goyon bayan Shugaba Buhari.

“Ko a lokacin da jam’iyyar APC ke sake sabunta rajistar mambobinta, ban shiga an yi hakan da ni ba.

“A yanzu din nan da nake zaune a gabanku, ban kasance mamba ga kowace jam’iyyar siyasa ba a fadin kasar nan.”