✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba na neman mijin aure – Zee-zee

Fitacciyar ’yar fim din Hausar nan Ummi Ibrahim wacce aka fi sani da Ummi Zee-Zee, ta musanta batun da wasu kafafen watsa labarai suka buga …

Fitacciyar ’yar fim din Hausar nan Ummi Ibrahim wacce aka fi sani da Ummi Zee-Zee, ta musanta batun da wasu kafafen watsa labarai suka buga  cewa tana neman mijin aure.
Ummi ta ce a matsayinta na fitacciyar jaruma, ta fi karfin ta fito kafafen watsa labarai tana neman mijin da zai aure ta, baya ga dimbin masoyan da ta ce Allah Ya ba ta, wadanda kuma ta bayyana cewa a shirye suke a kowane lokaci su aure ta.
A cewarta, ba ta ji dadin maganar ba, haka kuma cin fuska ne kai-tsaye a danganta ta da wannan batu. “A gaskiya ban ji dadin wannan magana ba. Ta yaya ma za a ce ina neman miji? Idan aure nake so ina da mazan da a shirye suke su fito su aure ni, don haka ba wani batun neman ma’auri da nake yi,” inji ta.
Aminiya ta gano cewa an dauki tsawon lokaci ba a ganin ’yar fim Ummi Zee-Zee a fina-finan Hausa, saboda tafiya hutun da ta yi kamar yadda jarumar ta shaida wa jaridar.
Jarumar dai ta bayyana cewa a yanzu haka ma tana nan tana shirye-shiryen dawowa harkar fim gadan-gadan, inda take shirya wasu manyan fina-finai. “Ina yi wa masoyana albishir cewa su sa ido a hanya, domin ina nan ina shirye-shiryen dawowa harkar fim din Hausa tsundum. Ina nan zan dawo da karfina, domin zan shirya wasu manyan fina-finai insha Allahu,” inji ta.