Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce har yanzu bai yanke shawawar tsayawa takarar shugaban kasa ba a babban zabe mai zuwa a shekarar 2023.
Kwankwaso ya bayyana haka ne cikin wata hira da ya yi da Sashen Hausa na DW a ranar Laraba, inda ya ce yana tattaunawa tare da tuntubar masu ruwa da tsaki don yanke hukuncin da ya dace.
- Najeriya A Yau: Me Sabon Mashawarcin Shugaban Kasa Kan Tattalin Arziki Zai Tsinana Wa Talaka?
- Za a fara yanke wa masu garkuwa da mutane hukuncin kisa a Filato – Lalong
Ya ce, “A wannan lokaci ba hanzari muke yi ba, don haka muna bibiyar komai a sannu, sannan muna neman shawarar wadanda suka dace kuma za mu yanke hukunci kuma mu sanar da mutanenmu.
“Muna da tarin magoya baya da suka isa mu yi kowace takara. Muna da mutane a ko’ina a Najeriya. Wasu na tunanin a Kano ko Arewa muke da magoya baya, amma ba haka abun yake ba, don muna da magoya baya a yankin Asiya, Amurka har da nahiyar Turai,” cewar Kwankwaso.
Kazalika, ya musanta rade-radin da ake na cewa shi da magoya bayansa na shirin ficewa daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC, inda ya ce babu wani abu mai kama da hakan.
“Batun sauya shekata zuwa APC an dade ana yin sa a lokuta mabambanta. Wannan ba shi ne karo na farko da hakan ta taba faruwa ba. Mutane da dama suna ta magana a kai, don dole ya zama abun farin ciki a ce kowa na magana a kanka. Wannan na nuna nagarta da jajircewar da muke da ita.
“A yanzu ba ni da masaniya a kan hakan kuma ban shiga tattaunawa da kowa ba don komawa APC. Wannan shi ne abin da zan iya cewa a yanzu,” kamar yadda ya bayyana.
Tsohon Sanatan ya ce siyasa na son yin aiki tukuru da jajircewa, wanda hakan zai sa mutum ya samu gogewa.