Mai Martaba Shehun Borno, Abubakar Umar Garba El-Kanemi ya ce Masarautar Borno ba ta taba samun wani rahoto a kan zargin sojoji da take hakkin Bil-Adama ba ko kuma wata matsala ta daban.
Shehun na Borno ya bayyana hakan ne a yayin da yake karbar bakuncin mambobin Kwamitin Bincike na Musamman kan Take Hakkin dan Adam a Ayyukan Yaki da Tayar da Kayar Baya a Arewa maso Gabas (SIIP-NE).
- ISWAP ta kashe Kwamandan Boko Haram Abu Zara da mayakansa 15 a Borno
- A kama duk mutumin da ya ki karbar tsofaffin kudi —Gwamnan Zamfara
El-Kanemi ya ce “dangantakar da ke tsakanin mu da sojoji tana da kyau kuma tana kara karfi da armashi matuka.
Ya kara da cewa, a matsayinsu na mutanen da ke kusa da talakawa, “ba mu taba samun wani rahoto ba dangane da zargin da ake yi wa sojoji kan zubar da ciki da kashe jarirai da Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya ruwaito a baya ba.
“A gaskiya ni da kuma abin da ya shafi Masarautar Borno, babu wanda ya taba zuwa wurina ya koka da irin wannan take hakkin dan Adam da ake zargin sojojin da yi.
“Ba mu sami wani mummunan abu game da sojoji ba kuma za mu ci gaba da tallafa musu matuka dangane harkokin tsaro wadda hakkin mu ne yin hakan,” in ji Shehun na Borno.
El-Kanemi ya ce “Game da abin da ya shafe mu, muna goyon bayansu 100 bisa 100 a yanzu da kuma ba za mu yi kasa a gwiwa ba.
Mai martaba ya bayyana yadda masarautar ta yi asarar rayuka da dama da suka hada da na sarakunan gargajiya sama da 200 a rikicin da kuma yadda ‘yan ta’addan suka mamaye kananan hukumomi 17 a cikin Jihar.
Ya kuma yaba wa sojojin da suka kwato kananan hukumomin tare da maido da zaman lafiya a Borno.
El-Kanemi ya yaba wa Hukumar Kare Hakkokin Dan Adam ta kasa (NHRC) da ta kafa kwamitin binciken take hakkin dan Adam.
Ya bukaci ta da ta yi adalci ga zarge-zargen tare da fallasa duk wani mai kokarin bata wa al’ummar kasar baki daya suna.
Tun da farko, Babban Sakataren Hukumar NHRC, Cif Tony Ojukwu wanda ya gabatar da mambobin kwamitin ga Shehu, ya ce sun je fadar ne domin neman goyon bayansa da kuma albarkarsa.
Ojukwu ya ce kwamitin yana da Alkalin Kotun Koli mai ritaya, Mai Shari’a Abdu Aboki a matsayin Shugaban Hukumar domin nuna irin muhimmancin da gwamnati ke da shi wajen gudanar da bincike.
A nasa jawabin, Mai shari’a Abdu Aboki wanda ya yi wa Shehu bayani kan batutuwan da kwamitin zai bincika, ya bukaci goyon bayan masu ruwa da tsaki da kuma hadin kansu dangane da wannan aiki mai muhimmanci da suka sa a gaba.
Kwamitin ya kuma ziyarci Hedikwatar Rundunar Operation Hadin Kai a Maiduguri, inda suka gana da jami’an rundunar kan abin da ke tafe da su.