✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba mu muka shirya zanga-zangar yaki da tsadar rayuwa ba —NLC

Ba NLC ce ta shirya zanga-zangar ba, kuma ba ta manta da ƙuncin rayuwa da ake ciki ba.

Ƙungiyar Ƙwadago ta Kasa NLC ta musanta rade-radin cewa ta janye daga zanga-zangar kasa da ake shirin gudanarwa a ranar 1 ga watan Agusta.

Cikin wata sanarwa da ta fitar a shafinta na X, NLC ta bayyana rahotannin a matsayin karya tare da cewa ba za ta iya janyewa daga zanga-zangar da ba ita ta shirya ba.

“Masu shirya zanga-zangar ta kasa ce kawai za su iya yanke shawarar janyewa ko ci gaba da zanga-zangar,” in ji NLC.

Sanarwar ta bayyana cewa “NLC tana da hanyoyi musamman hanyoyin yanke hukunci kan jagoranci wanda ayyukanta na masana’antu kamar zanga-zangar ke bi kafin a gudanar da irin wadannan ayyukan.”

NLC ta kuma nuna goyon bayanta ga zanga-zangar da ake shirin gudanarwa, tare da amincewa da matsin tattalin arzikin da ‘yan Najeriya ke fuskanta saboda manufofin gwamnati.

“Kasancewar NLC da cewa ba ita ta shirya zanga-zangar ba, hakan ba ya nufin kungiyar ta manta da halin ƙuncin rayuwa da ‘yan Najeriya ke ciki sakamakon munanan manufofin tattalin arziki na gwamnati,” in ji kungiyar ta NLC.

NLC ta buƙaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya shiga tattaunawa da jagororin zanga-zangar domin biyan bukatunsu inda ta ba da shawarar a guji amfani da ƙarfi wajen mayar da martani ga rashin jin dadin jama’a.

Tuni dai shugaban na Nijeriya ya roƙi ‘yan kasar da su janye shirin zanga-zangar da suke niyyar yi a farkon watan Agusta mai kamawa.

Ministan Watsa Labarai, Mohammed Idris ne ya shaida wa manema labarai hakan a fadar gwamnati a Abuja bayan kammala ganawarsa da shugaban kasar.

Ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya nemi masu shirya zanga-zangar da su dakatar da ita su jira su ga matakin da zai ɗauka a kan ƙorafe-ƙorafensu.

Roƙon na Shugaba Tinubu na zuwa ne a yayin da ake ta ci gaba da batun gudanar da zanga-zangar da aka yi wa take da ‘EndBadGovernance’, a fadin ƙasar musamman ma a shafukan sada zumunta.