Rundunar ’yan sanda a Jihar Kaduna ta musanta cewa tana da hannu wajen sakin wasu daga cikin ababen zargin da take kamawa kan ta’adar garkuwa da mutane don neman kudin fansa.
Kakakin rundunar ASP Mohammed Jalige ya musanta zargin a lokacin da yake zantawa da Aminiya ta wayar tarho kan yawan zargin ’yan sanda da ake yi bayan sun gabatar da wadanda ake tuhuma a gaban kotu.
- Osinbajo ya tafi wakiltar Buhari a taron ECOWAS a Ghana
- ’Yan sanda sun kama dan da ya kashe mahaifinsa saboda ya ci gado
Jalige ya ci gaba da cewa dukkan mai laifi da ’yan sanda suka gabatar a gaban kotu ko shakka babu sauran aikin ya koma hannunta wadda ita ce alhakin dauri ko saki ya rataya a wuyanta.
A cewarsa, “’yan sanda ba sa kai mai laifi ko wanda ake tuhuma gidan yari saboda kotu ce kadai doka ta bata wannan iko.
“Saboda haka ya kamata Jama’a su yi kokarin fahimtar yadda hurumin ’yan sanda yake da kuma hurumin kotu watau bangaran shari’a.
ASP Jalige ya kuma bayyana takaicinsa bisa yadda ake alakanta rundunar ’yan sanda da sakin ’yan ta’adda bayan sun gurfanar da su a gaban kotu, “a maimakon a kalli kotu sai hankalin jama’a ya karkata ga ’yan sanda cewa su ne suke sakin masu laifi.”
Ya bayar da misali da cewa, “akwai wanda suka gabatar da shi a gaban kotu kuma ta turashi zaman ajiya amma sai gashi an ganshi yana harkokinsa a cikin jama’a ba tare da an yi masa shari’a ba.
“Akwai wadanda suka kashe dan sanata Bala Bin Na Allah, kuma rundunar ’yan sandan jihar Kaduna ta samu nasarar kamasu, amma abin mamaki dukkansu an taba kamasu da laifin fashi da makami kuma aka gabatar da su a gaban kotu har an yake musu hukunci na tsawon shekaru kusan hudu zuwa biyar, gwargwadon laifin da suka aikata, amma sai gashi ko wata bu suyi ba mun sake kamasu da laifin kisan gilla, a nan wanene ya sake su?”
Shin laifin na ’yan sanda ne ko kotu?
ASP Mohammed Jalige ya ce, “a binciken da muka yi sai gashi an yi amfani da wani Alkali an bashi kudi naira dubu 70 aka sako su, shi ne bayan fitowarsu da kwana uku suka je suka kashe dan sanata Bala Bin Na Allah.
“A game da wani mutum mai suna Bashir wanda ke zaune a yankin Wusasana garin Zariya wanda kotun Majistare da ke Kofar Fada Zariya ta daure shi shekara 14 ba tare da zabin tara ba bisa laifin garkuwa da mutane, sai ga shi bayan wata daya ya fito yana ci gaba da harkansa.
“Haka shi ma wani wanda ya hada baki da masu garkuwa da mutane mai suna Abubakar Halliru da ke Unguwar Magumai a Zariya.
“Bayan sun sace ’yar uwarsa da nufin su kasheta saboda ta bashi aron kudi har Naira miliyan daya da dubu dari 400, kuma ta kwashe kusan wata biyu a hannunsu, kafin Allah ya kubutar da ita daga hannunsu, shi ma ’yan sanda sun gurfanar da shi a gaban kotu inda tun kafin a kai ga kammala shari’a sai gashi an sake shi yana harkokinsa a cikin jama’a.
“Wannan ne ya janyo hoton bidoyon kama shi yake ta yawo a kafofin yada labarai na zamani ana zargin ’yan sanda cewa sun saki mai laifi irin wannan, ba tare da binciken yadda aka sake shi ba.
Wakilinmu ya ruwaito cewa, wadannan bayanai da ASP ya yi na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da korafe-korafe da kum zargin da al’umma ke yi wa ’yan sanda a duk lokacin da suka kama masu manyan laifuka irin na ta’addanci.
Kazalika, ASP Jalige ya bayyana mamaki kan zargin da Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Tarayya ya yi na cewa rundunar ’yan sandan jihohin Kaduna da Nasarawa da Filato, suna sakin ’yan ta’adda wadanda ke kashe mutane ko garkuwa da su a duk lokacin da aka kama su.
ASP Jalige ya bayyana takaicinsa matuka a kan wannan babban zargi la’akari da cewa Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar ya yi shi ne a zauran majalisa wadda hakan ya daga hankalin manyan kasa da kuma al’ummomi da dama.
Ya ce “kamata ya yi mai girma shugaban masu rinjaye ya gudanar da bincike kafin ya gabatar da koken nasa a zauren majalisa.
ASP Mohammed Jalige, ya ce ya kamata a rika binciken batutuwa kafin a bayyana wa jama’a saboda a lokuta da dama ana daukan tanki ana barin jaki.