✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba mu gamsu da kalaman dattawan Arewa ba

Assalamu alaikum Editan Aminiya. Kalaman Kungiyar Dattawan Arewa (Northern Elders Forum) da suka ce wai babu wani abin ci gaba da Shugaba Muhammadu Buhari ya…

Assalamu alaikum Editan Aminiya. Kalaman Kungiyar Dattawan Arewa (Northern Elders Forum) da suka ce wai babu wani abin ci gaba da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa yankin Arewa tsawon shekara hudu a karagar mulki don haka ba za su goya masa baya a zaben 2019 ba abin takaici ne. Haba dattawanmu na Arewa yanzu duk irin ayyukan ci gaba da Shugaba Buhari ya shimfida a Arewa shi ne za ku ce haka? To ku sani mu al’ummar Arewacin Najeriya mun dauki wadannan kalamai naku tamkar wani soki-burutsu, ku dai kawai ku fito ku fadi gaskiya don kun ga Shugaba Buhari ya toshe dukan wasu kofofin da kuke samu ku yi cuwa-cuwarku ce, shi ya sa kuka fito ta nan. Don haka ku sani mu al’ummar Arewa masu tikitin kada kuri’a a hannu wallahi har gobe kuri’unmu na Shugaba Buhari ne, kuma muna tare da shi dari bisa dari domin mun gamsu da irin kamun ludayinsa. Dan haka lokaci kawai muke jira

 

Dalibi a Sashen Noma da Kiwo Jami’ar Maiduguri, Baba Gana Alhaji Nuchiya Wachakal, da Grema Gress Wachakal, da Kuma Haruna Boda Inkaibo, 08132511818, 08024602506.